Babangida Aliyu shirgegen makaryaci ne, kuma mayaudari – Jonathan

0

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karyata tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, da ya ce wai shi Jonathan din ya karya alkawadin da ya dauka wa gwamnonin Arewa shi ne ya sa ya fadi zabe a 2015.

Daya daga cikin tsoffin hadiman Jonathan, Reno Omokri, wanda shine ya sanya wa martanin Jonathan hannu, ya ce Babangida Aliyu na surutai ne kawai don a ruka yi da shi a siyasa amma shirgegen makaryaci ne.

” Babu wani yarjejeniya da aka yi da ni a baya da gwamnonin Arewa 19 kan takara da na yi. Ba a taba yin haka da ni ba. Amma yanzu Aliyu ya wage baki yana yanko karya kawai don ya samu madafa a siyasance.

” Sule Lamido da kansa ya fadi cewa ba a taba yin haka ba. Hasalu ma shine Aliyu ya tausa idan na gwaggwale wa Jonathan ido a wancan lokacin.

Haka shima gwamnan Filato, Simon Lalong ya karyata Aliyu, yana mai cewa ba a taba zama don amincewa da yarjejeniya irin haka ba.

Babangida Aliyu

A wata sanarwar da tsohon gwamnan jihar Neja Babanhida Aliyu ya rabawa manema labarai, yace gwamnonin Arewa sun dauki matakin juya wa tsohon shugaban kasa Jonathan baya ne saboda karya alkawarin da dauka cewar ba zai tsaya takara ba bayan kammala wa’adin tsohon shugaban kasa Umaru Yar’adua da kuma sama nasarar zaben 2011.

Babangida ya ce gwamnoni sun marawa Jonathan baya lokacin da Yar’ Adua ya rasu da kuma takarar sa ta shekarar 2011, amma hakikancewar sa cewa zai zarce a shekarar 2015 ga ba dayansu su gwamnoni suka mo nuna masa bai Isa ba.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar PDP a karamar hukumar Chanchaga ta dakatar da tsohon Gwamnan saboda abinda ta kira zagon kasa da kuma wasu harkoki da suka sabawa Jam’iyar ta su.

Share.

game da Author