‘Yan Najeriya sun fada cikin halin kakanikayi da gararamba bayan bankunan Najeriya sun dakatar duk wani mai layin MTN iya siyan katin kira ta asusun ajiyar sa na banki tun daga ranar Alhamis.
Bayan mutane sun kasa iya siyan katin kira ta bankunan su aka fara korafi da neman bayanai daga bankunan da kamfanin sadarwar MTN. MTN ta aika wa masu amfani da layin kiran cewa daga yanzu duk mai son kira da layin MTN ya garzaya shagunan siyar da kati kai tsaye da kuma irin na bakin hanya ya kai tsaye.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an samu tankiya ne a tsakanin MTN da bankuna wurin raba ribar kudaden da ake cirewa idan aka siya katin.
Hakan ya sa bankunan kasar nan suka dakatar da ci gaba da harkar siyan katin kira na kamfanin MTN yanzu har sai sun warware matsalar dake tsakanin su.
Yan Najeriya da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun nuna damuwar matuka akan haka.
” Na shekara ya fi biyu da na siya katin kira ta hanyar siyan kati a waje. Ta waya nake yi, yau kuma gaba daya sai na rude da babu ta hanyar banki. Sai da na fita na shiga gari kafin nan na siya katin da na yi kira da shi.” inji Mohammed Nasir.hammed Nasir.
Discussion about this post