Gwamnatin Tarayya ta umarci GoTv da Startimes su bude wa ’yan Najeriya tashoshin su kyauta

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta umarci GoTv da Startimes su karkata zuwa ga bude wa ’yan Najeriya tashoshin talbijin din da ke karkashin kamfanonin su kyauta, ba tare da biyan ko sisi ba.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a Abuja, inda ya kara da cewa wannan umarni ya zo ne sanadiyyar komawa tsarin DSO.

Najeriya dai ta bada wa’adin nan da 29 Ga Afrilu sauran jihohi 31 su gaggauta komawa sabon tsari na zamani, DSO, wato Digital Switch, na nufin komawa tsarin zamani daga tsarin ta-ci-barkatai ko tsohon yayi.

Jihohin farko da su ka fara sakin tsarin tsohon yayi (analogue) zuwa sabon yayi (digital), sun hada da Filato, Kaduna, Kwara, Osun da Enugu, sai kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Minista Lai ya kara a cewa dokar Najeriya ta amince da bin tsari daya tal wajen sadarwa ta kafafen talbijin a karkashin masu bada lasisi biyu, wato ITS da kuma Pinnacle Communications.

A kan haka ya ce laifi ne babba da kuma kauce wa sharudda ganin har yanzu kamfanonin sadarwa na GoTv da Startimes na amfani da tsarin watsa tashoshin da kowanen su ya ga dama.

“Saboda haka mun umarci Hukumar Kula da Gidajen Talbijin da Radiyo ta Kasa (NBC) ta umarci GoTv da Startimes su gaggauta rajista da tsarin da ake a kai ko dai su dora tashoshi a karkashin Pinnacle ko kuma a karkashin ITS.

Ya ce idan su ka yi haka, ‘yan Najeeiya za su samu damar kallon tashoshi masu yawan gaske a karkashin GoTv da Startimes.

Share.

game da Author