Matawalle zai koma APC

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya gama shiri tsaf domin komawa jam’iyyar APC a jihar Zamfara.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa idan ba wani sauyin bazata aka samu ba, Matawalle zai bayyanar komawarsa jam’iyyar APC ranar Talata.

Sai dai kuma ba a nan gizo ke sakar ka, tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya bayyana cewa ba zai yi zaman jam’iyya daya da Matawalle ba.

Akwai yiwuwar idan Matawalle ya canja Sheka, ya shiga APC Yari zai koma PDP ko wata jam’iyyar.

Kamar yadda jaridar ta wallafa, tsohon gwamna Ahmed Yerima na daga cikin wadanda suke zawarcin Matawalle ya dawo APC domin su karya karfi da babakeren da Yari yayi wa jam’iyyar APC a jihar.

Yari ya hana kowa sakat a APC a jihar. Shine wuka shine nama, ko ka yi da shi wato kabi yadda ya ke so ko ka fice daga jam’iyyar.

A kwanakin baya shugaban jam’yyar na Kasa, Mala Buni ya sasanta tsakanin tsohon gwamna Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Wannan abu na nufin akwai cakwakiya nan gaba a jam’iyyar, domin kuwa idan Matawalle ya koma APC, gaba daya dole kowa ya bishi a matsayin shugaban jam’iyya a jihar harda shi kanshi Yari idan har yana so ya ci gaba da zama a APC, wanda shi kuma ba zai so haka ba domin ba a ga maciji a tsakanin su.

Ba Yari ba kawai, an ya za a daisaita da sanata Marafa da Matawalle a jam’iyya da ya kuwa, ganin sune yan asali matawalle zuwa yayi.

A wani bngaren kuma, tsohon gwamna Yarima da na shi tawagar suma wani rawa za a a taka da su?

Tsakanin Matawalle da PDP

Gwamna Matawalle ya dade yana kuka da yan jam’iyyar sa wato PDP kan rashin nuna masa shima nasu ne. Ya dade yana fadin cewa su ne suka fi nuna masa banbanci da nuna halin ko-in-kula a duk lokacin da wani abu ya shafe shi a jihar.

“Ga shi ko gabarar da ya afka wa kasuwa, APC da makarrabanta sun sanar mana da shirin garzayowa yi mana jaje, amma jam’iyyata, PDP, sam babu abinda ya dame su akai.”

Yanzu dai muna sa ido mu gani Allah ya kai mu talata.

Share.

game da Author