Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa babu abinda ya dada shi da kasa, kan wani bidiyo da ake ta watsa wa a shafukan yanar gizo, da ke nuna shi yana bayanin gazawar gwamnatin Goodluck Jonathan a harkar tsaron kasar nan a 2014.
Babban maiba gwamna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin watsa labarai, Muyiwa Adekeye ne ya bayyana haka a wata takarda mai tsawon gaske da ya fitar ranar Talata a Kaduna.
” Dalilan da ya sa El-Rufai ya yi wadannan kalamai a wancan lokacin shine ganin ita wancan gwamnatin bata ma yarda ne wai an sace daliban makaranta ba. Ta rika karyata abun tana maida shi siyasa.
Adekeye ya ce wannan shine babban dalilin da yasa irin su gwamna El-Rufai a wancan lokaci suka fito suna kalubalantar gwamnatin sa ta san yadda zai yi ya ceto wadannan dalibai na Chibok, ko ta halin kaka domin lallai an fa sace su, wanda gwamnatin bata yarda ba a lokacin.
” Yan zu shine wasu suka garzaya baya suna
Zakulo wadannan bidiyo da aka dauka domin wata manufa ta su. Su nuna wa duniya wai El-Rufai ya gaza. Amma kuma shi bai gaza ba domin wancan lokaci da banbanci da yanzu.
” Ya kamata mutane su sani cewa daga 2014 zuwa yanzu abubuwa da yawa sun canja. Biyan kudin fansa bai haifar wa wadanda ke biya da mai ido ba. Abin ya kazanta harkar yin garkuwa da mutane ne. Babu cigaba da sauki da ka aka samu. Wannan shine dalilin da ya sa gwamnatin El-Rufai ba ta fada wannan tarko ba na biye wa biyan kudin fansa da sai dai ya kara musu karfi ba gurgunta su ba.
” Mu a namu bangaren muna nan muna tattaunawa da gwamnatin tarayya kan matsalar tsaro da ake fama da shi. Maimakon a rika jira sai mahara sun kawo hari sannan a rika tattarewa, binsu yakamata a rika yi har inda suke ana dagargaza su. Wannan shine kawai zai sa su shiga taitayin su kuma su dakatar da ayyukan hare-hare da suke yi.
” Gwamnatin jihar Kaduna na mika sakon jajenta ga iyaye da yan uwan yaran makarantan da aka kashe, sannan kuma gwamnati na nan tana ci gaba da zakulo hanyoyin da zasu taimaka wajen kawo matsalar tsaro a jihar da kasa baki daya.