Uwargidan jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, Sanata Remi Tinubu, ta tir da kalamansanata Adeyemi Smart, wanda yayi a zauren majalisar Dattawa ranar Talata yana kalubalantar shugaban Kasa ya gane da tsananin matsalar tsaro da ya dirkako kasar nan.
Tinubu ta rika ce masa, ya yi shiru ya dai na magana a lokacin da yake jawabi a zauren majalisar dattawa.
” Ka yi wa mutane shiru, ko kaima dan PDP ne? Me yasa za ka rika fadin haka kana dan APC, kura da fatar akuya”. Haka ta rika cewa a lokacin da yake jawabin sa.
Sai dai sanata Smart, bai saurareta ba, ya ci gaba da jawabin sa, har yana cewa matsalar tsaro a kasar nan ya wuce wandaa aka yi fama da shi lokaci yakin basasa, da aka a Najeriya.
Sanata Smart Adeyemi, wanda ya barke da kuka a lokacin da yake jawabi, ya yi kira ga sanatocin da su cire siyasa kowa ya tattaro hankalin sa wuri daya a sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari halin da kasa ke ciki.
” Gaskiyar magana shine Najeriya ta shiga halin kakaknikayi game da matsalar rashin tsaro wanda bata taba fadawa ciki ba. Wannan matsala fa ya kai intaha, dole mu ajiye siyasa a gefe mu fada wa kan mu gaskiya. Ko ina ya dagule, babu tsaro.
” Yau mutum bashi da damar yin tafiya a Najeriya, ko ina ana cikin matsala na tsaro. Ina zamu saka kan mu. Abu ya kai ga hatta ana
kakkafa tutoci a wasu ya kunan kasar nan.