Jami’an SSS sun shafe sa’o’i takwas tsare da fittacen dan siyasa Usman Bugaje, wanda su ka tsare saboda wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na AIT.
Majiyar kusa da Bugaje ta sanar cewa ya kai kan sa ofishin SSS na hedikwatar su da ke Abuja, ranar Laraba wajen karfe 10 na safe.
Bugaje dai Bakatsine ne da ya ki karbar tayin mukamin jakadan Najeriya, wanda Shugaba Muhammadu Buhari yay i masa cikin 2016.
An tsare shi ana yi masa tambayoyi tsawon sa’o’i takwas a ofishin SSS, Hedikwatar Abuja.
An shaida wa PREMIUM TIMES cewa an saki Bugaje ya tafi gida wajen karfe 7 na yamma bayan an bayar da belin sa a ranar Laraba.
Wani makusanci Bugaje ya shaida wa PREMIUM TIMES cea an gayyace shi ofishin SSS din tun makonni biyu da su ka gabata, bayan an yi wata tattaunawa da shi a gidan talbijin na AIT, a Abuja.
“An yi hira da Bugaje a wani shiri inda ya fito har sau biyu cikin makonni biyu da su ka gabata a Gidan Talbijin na AIT.
“Bayan fitowar biyu da ya yi ne sai SSS su ka gayyace shi, domin wai ya bayar da karin haske a kan wasu kalamai da ya yi a cikin tattaunawar da aka yi da shi a AIT.”
Bugaje kusa ne daga cikin dattawan Arewa ‘yan boko kuma ‘yan siyasa.
Ya yi aiki tare da gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Cikin 2016 Buhari ya nada shi jakadan Najeriya, amma ya watsar ya ce ba ya so, tun kafin a rasa masa sunan kasar da za a tura shi.
Ya ce ya watsar da tayin ne domin ya na da wani shiri na kafa wata tafiya domin ceto Arewacin Najeriya, tafiyar da ya kira “Arewa Research and Development Project (ARDP).”
Kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na SSS, Peter Afunanya, ya ci tura, saboda bai dauki waya ko amsa sakon ‘tes’ ba.
Discussion about this post