ALAKA DA BOKO HARAM: Shin da gaske ne kasar Amurka ta dalla wa sheikh Pantami hasken wutar zargi

0

A ranar 12 ga Afirilu wata jarida mai suna Independent ta wallafa labarin cewa wai kasar Amurka ta sa wa Sheikh Ibrahim Pantami ido kan zargin sa da alaka da kungiyar Boko Haram. Jaridar ta ce wai hukumar tsaro na sirri a Amurka ta na bibiyar ayyukan sa sau da kafa a dalilin wannan zargi.

Haka kuma a wani zargin, wani dan jarida mai zaman kansa, David Hundeyin ya saka wani bodiyon dake nuna Pantami da sheikh Yusuf a lokacin da suke wani mukabala mai zafi, wand shi Pantami ke kalubalantar wannan akida ta kungiyar Muhammed Yusuf.

PREMIUM TIMES ta gudanar da binciken kwakwaf inda wakilinta ya bi diddigin wadannan rahotanni da kuma bayannan domin binciko gaskiyar abinda yake game da wannan zargi da korafi.

Da farko dai babu wata hujja da aka bayar cewa wai Amurka na bibiyar sheikh Pantami, wai har sun dalla masa hasken wuta na musamman kan zargin wai yana da alaka da Boko Haram a Najeriya.

Haka kuma ita kanta inda jaridar da ta wallafa wannan labari ta shirga karya ne cewa wai ta samo shi a wani taska ce ta sirri, bincike ya nuna cewa babu irin wannan taska ko kuma kundin labarai kamar yadda ita jaridar ta ce a nan ta kwakulo hujjojinta.

Tuni dai jaridar ta cire wannan labari a shafinta.

Haka kuma wannan bidiyo da aka rika yadawa dake nuna sheikh Pantami da Muhammad Yusuf wai suna zaman nishadi na abokantaka shima karya ne.

Wannan bidiyo ne da ke nuna Pantami a lokacin da yake mukabala mai zafi tsakaninsa da Muhammed Yusuf.

A wannan mukabala, sheikh Pantami na kalubalantar Muhammad Yusuf tare da bashi wasu hujjoji masu karfin gaske game da inganci karatun Boko a Musulunci wanda manyan malamai da dama a duniya suka yi ittifaki akai cewa ya hallata.

Amma kuma wasu suka karkatar da ma’anan wannan bidiyo saboda wata manufa tasu suka yi mata mummunar fassara saboda wani mummunar ra’ayi na su.

PREMIUM TIMES ta nemi bayanai daga bakunan mawallafan jaridun da suka wallafa wannan labarin kage domin ji ta bakunan su amma duk sun ki cewa komai akai, duk wanda muka nemi ya ce wani abu sai ya sulale ya ce zai nememu gaba kadan.

Sannan kuma ita kanta ma’aikatar tsaron Amurkan da suka ce wai sune suke zargin Pantami da alaka da Boko Haram, babu ita kwata-kwata a jerin hukumomi da ma’aikatun tsaron Amurka, karya ce kawai da kagen iska.

A karshe dai abinda muka gano bayan bincike da PREMIUM TIMES ta yi tun daga nan gida Najeriya har zuwa can Amurka din domin tantance gaskiyar wadannan zargi, ta gano ita kanta kasar Amurkan ma bata san da labarin ba, sannan babu wani abu na zargi da ya hada wata hukumar tsaron kasar da Pantami. Kuma wannan hukuma da aka ce wai ita ce ke bibiyar Pantami babu hukuma irin haka a kasar Amurka.

Share.

game da Author