Da kuri’u ya kamata a rika cin zabe ba a kotuna ba –Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya yi kira da a karfafa dokokin zabe, ta yadda sai da kuri’a kadai za a iya bayyana wanda ya yi nasara, ba a kotu ba.

Jonathan ya nemi a haramta wa kotuna bayyana sakamakon wanda ya yi nasara.

Jonathan ya kara da cewa nagartaccen tsarin da aka sani shi ne hukumar zabe ce ke da alhakin bayyana wanda ya yi nasara, su kuma kotuna, aikin su kawai ko dai su bayyana sahihancin nasarar wanda INEC ta bayyana ya yi nasara, ko kuma idan akwai hujjar soke zaben, sai ta soke ta bada umarnin sake zabe a inda ya zama dole a sake.

Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan ya yi wannan bayani a ranar Litinin, yayin ganawa da manema labarai, a wata ziyara da ya kai gidan talbijin din TOSTV da ke Abuja.

“Tuni na yi bayani karara a kan wannan batu cewa kuri’un jama’a ne ya kamata su rika bayyana sakamakon zabe, ba wai a kotu za a rika bayyana wanda ya yi nasara ba. Kada kotuna su rika zabar mana ko dara mana shugabanni na siyasa. Wannan aikin kuri’un da jama’a suka jefa ne, ba aikin kotuna ba.”

Yawancin sakamakon zabuka a Najeriya, duk kotuna ne a karshe ke bayyana wanda ya yi nasara, saboda rigingimun rashin amincewa daga wanda aka kayar da kuma zargin dimga magudin zabe.

Babban misalin da ya fi daure kan jama’a a kasar nan, shi ne yadda Kotun Koli ta soke zaben Emeka Ihedioha na Jihar Imo daga PDP a matsayin sa na gwamnan Imo, bayan ya shafe watanni masu yawa a kan mulki.

Amma maimakon a bai wa wanda ya zo na biyu, sai a ka bai wa wanda ya zo na uku, wato Hope Uzodinma na APC, wanda a yanzu ke kan mulkin jihar.

Har yanzu akwai masana da masu sharhin da ganin cewa fashin kujerar gwamna Kotun Koli ta yi daga PDP ta bai wa dan takarar APC, wanda kuri’un sa ko kusa ba su yi daidai da yawan wanda ya zo na biyu ba, ballantana su kusa yawan wanda ya zo na daya.

Share.

game da Author