ZAMFARA: Yadda Mahara suka cinna wa kauyuka wuta suka nausa daji da yara kanana da mata

0

A cikin murnar dawo da daliban makarantar Jangebe da mahara suka yi garkuwa da, wasu riakakkun yan bindiga sun sake cusa wa mazauna kauyen Ruwan Tofa, daje karamar hukumar Maru, jihar Zamfara bakin ciki a zukatan su ranar Laraba.

Wani mazaunin garin Ruwan Tofa ya bayyana wa wannan jarida cewa mutanen garin Ruwan Tofa sun gamu da bala’i a wannan hari, domin tun daga isowar yan bindigan garin, sun fara ne da cinnawa rumbunan abinci wuta da gidajen mutane.

” Daga nan sai kowa ya fito, mata da yara a ka shiga guje-guje. Suka tattare mutane musamman mata da yara kanana suka bausa da su cikin daji.

Majiyar ta mu ya ce ba zai iya fadin adadin yawan wadanda aka tafi da su ba, amma da dan karan yawa.

Idan ba a manta ba, a ranar Alhamis gwamnatin Jihar ta saka dokar hana walwala a garin Jangebe, bayan matasa sun fito zanga-zanga inda suka rika yi wa jami’an gwamnati ruwan duwatsu a lokacin da su ke ganawa da iyayen daliban da aka ceto daga hannun mahara.

Haka kuma shuma gwamnan jihar Bello Matawalle ya kalubalanci hukuncin da gwamnati ta dauki kan dakatar da shawagin jiragen sama a samaniyar jihar Zamfara.

Matawalle ya ce ” A zuba a gani ko gwamnati zata iya kawo karshen hare-haren yan ta’adda, tunda bata tare da shi a maganan yin sulhu.

Share.

game da Author