Sojojin saman Najeriya sun yi dagadaga da kasurgumin dan bindiga Rufai Maikaji, da ya addabi Birnin Gwari, jihar Kaduna

0

Kwamishina Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, ya yi karin haske kan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu a yankin dazukan Birnin Gwari da kewaye, inda suka kashe kasurgumin dan bindiga da makarraban sa a wani hari da suka kai ranar Alhamis.

Wannan dan bindiga da ya addabi mazauna dazukan yankin Birnin Gwari, Rufai Maikaji ya sha wuta daga sojojin saman Najeriya a lokacin da suka gano maboyar sa.

” An rika yi masa luguden wuta daga sama babu kakkautawa har sai da aka gama da shi da wasu yan bidiga masu yawa a dajin.

Rufai Maikaji ya rika gallaza wa mazauna kauyukan da ke kewaye da Birnin Gwari babu kakkautawa, tare da kai hari a duk lokacin da ya so. Ya kashe na kashe sannan ya arce da wasu cikin kungurmin daji.

Matafiya a wannan hanya ma ba su tsira ba domin da shi Magaji da makarraban sa a kusan kullum sai sun tare hanya sun kwashe jama’a. Wanda kwanakin sa suka kare kuma su kashe shi.

Aruwan ya ce bincike da aka gudanar sun nuna cewa shi, wannan dan bindiga da abokansa ne k hare hare a yankin Iyatawa, Garke, Kumfa, Bakali, Karau-karau and Galadimawa, Anaba, Kerawa, Hashimawa, Sabon Birni, Buruku da kuma wasu kautuka da garuruwan karamar hukumar Chikun.

Share.

game da Author