Hanyoyin 10 da za a kiyaye don gujewa cutar dake kama maran mutum.
Cutar dake kama maran mutum cuta ce dake kama da cutar sanyi dake cutar da mafitsara, mara da kodar mutum.
Cutar ta fi kama mata fiye da maza.
Alamun cutar sun hada da yin fitsari da jini, rika jin zafi wajen yin fitsari ko lokacin yin jima’i, amai, gaban mutum zai rika kaikayi da fitar da ruwa mai wari, ciwon kafa, yawan jin gajiya, rashin iya yin fitsari da sauran su.
Maganin ‘Antibiotics’ na warkar da ire-iren wadannan cututtuka.
Yadda cutar ke ciga jikin mutum
1. Yawan barin fitsari na taruwa a mara.
2. Rashin tsaftace jiki musamman al’aura.
3. Amfani da ban dakin da bashi da tsafta.
4. Rashin shan ruwa yadda ya kamata.
5. Rashin saka kaya masu tsafta a al’aura.
Hanyoyi 10 da za a kiyaye don kare kai daga kamuwa da cututtukan da ke haddasa ciwon mara da gaban mace ko namiji
1. A rika shan kofin ruwa akalla takwas a rana.
2. A daina bari fitsari na taruwa a mara.
3. A rika yin fitsari kafin ko bayan jima’i.
4. A rika amfani da kananan wanduna da aka saka su da auduga idan za a kwanta barci.
5. Yin tsarki bayan anyi fitsari na taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.
6. Mata su guji fesa turare a gabansu.
7. Mata su guji amfani da dabaran bada tazaran haihuwa na ‘Spermicide’
8. Maza su guji amfani da kororo roba dake dauke da sinadarin ‘spermicidal lubrication’.
9. A rika cin abincin dake kara karfin garkuwar jiki domin samun kariya daga kamuwa da cuta.
10. A rage yawan wanka na gurza jiki a kullum, maimakon haka a yawaita watsa ruwa ne a jiki.