‘Yan Najeriya na rigerigen yin rajistan amincewa da yin alluran rigakafin Korona – Bincike

0

Kafin allurar rigakafin Korona ya dira Najeriya, mafi yawan wadanda aka tattauna da su don jin ra’ayoyin su sun ce ba su da ra’ayin yin rigakafin.

Babban abinda ya sa ba za su yi ba kuwa shine wai basu yarda da cutar ba, ballantana rigakafin cutar.

Sai dai kuma tun bayan da aka fara yi wa mutane harda shugaban kasa da mataimakin sa rigakafin cutar, sai aka fara tururuwan zuwa cibiyoyi da shafukan da ake rajistan yinrigakafin cutar.

Gamnati na bukatar ta tsananta yawar wa mutane kai game da alfanun yin rigakafin wanda hakan ya karanta matuka.

A wasu kautukan ma har yanzu akwai wadanda basu san rigakafin ya zo kasar nan ba har an fara yi wa wasu. Wasu ma har yanzu basu yarda da cutar ba.

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna yadda mutane ke kara yarda da yin allurar rigakafin.

Jami’ar ‘Imperial College London’s Institute of Global Health Innovation (IGHI)’ da Kamfanin gudanar da bincike ‘YouGov’ suka gudanar da wannan binciken akan mutum sama da 13,500 a kasashe 14 a duniya daga ranar 8 zuwa 21 ga watan Fabrairu 2021.

Binciken ya gudana a kasashen Australia, Britain, Canada, Denmark, France, Germany, Israel, Italy, Japan, Netherlands, Norway, Singapore, South Korea, Spain da Sweden.

A kasar Britaniya mutum kashi 77 bisa 100 sun tabbatar da za su yi allurar rigakafin sannan ko kadan mutanen basa fargaban samun matsaloli bayan sun yi rigakafin.

Korona a Najeriya

Sakamakon gwajin Korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na wannan mako ya nuna cewa mutum 2,382 suka kamu da cutar sannan mutum 47 suka mutu a sanadiyyar cutar daga ranar litinin zuwa Juma’a, 5 ga Maris.

An yi wa mutum 1,544,008 gwajin cutar a kasar nan. Daga ciki mutum 158,042 sun kamu.
Zuwa yanzu mutum 19,063 na killace a wuraren da ake kula da waɗanda suka kamu, an sallami mutum 137,025. Mutum 1,954 sun mutu.

Jihar Legas, Abuja, Filato, Kaduna, Oyo, Rivers, Edo, Ogun ne suka fi yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.
Zuwa yanzu yaduwar cutar ta fara raguwa haka kuma mutuwa daga cutar ya fara raguwa a kasan.

An fara yi wa jami’an lafiya allurar rigakafin korona a Abuja

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA ta fara yi wa jami’an lafiya dake aiki a asibitin ƙasa a Abuja allurar rigakafin cutar korona ranar Juma’a.

Shugaban kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kare kiwon lafiyar jami’an lafiya ganin sune ke kula da marasa lafiya a asibitoci.

Wani likita mai suna Cyprian Ngong da wasu jami’an lafiya uku aka fara yi wa rigakafin Korona a kasar nan.

A ranar Talata ne rigakafin Korona miliyan 4 suka iso kasar nan.

Shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaɗuwar cutar Korona a Najeriya Boss Mustapha, ministan Lafiya, Osagie Ehinare, da wasu jami’an gwamnati ne suka tarbi isowar maganin daga kasar Indiya a filin jirgin dama na Abuja.

Tuni har an yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakin sa, Yemi Osinbajo rigakafin cutar a fadar gwamnati ranar Asabar.

Share.

game da Author