Shugaban Hukumar Hana Sha da Tu’ammali da Kwayoyi ta (NDLEA) Kasa, Buba Marwa, ya bayyana rashin jin dadin yadda ake ci gaba da karin samun yawan masu hada-hada da fataucin miyagun kwayoyi a Jihar Lagos.
Marwa ya bayyana cewa akalla mutum milyan 4.5 na hada-hadar saye, sayarwa, fatauci da safarar muggan kwayoyi a Jihar Lagos.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kai ziyarar gani-da-ido a ofishin NDLEA na Lagos, inda ya ce dole sai an tashi tsaye an dakile harkar tu’ammali da muggan kwayoyi a Lagos da kasar nan baki daya.
Sannan kuma ya kara da cewa kashi 30 bisa kashi 100 na masu shan muggan kwayoyi a kasar nan, duk a Lagos su ke.
“A kasar nan, an yi kiyasin cewa akalla mutum milyan 15 na hada-hadar muggan kwayoyi a kasar nan. Kuma mutum milyan 4.5 din su duk a Lagos su ke.”
A ziyarar wadda ya kai ta kwanaki uku, Marwa ya umarci zaratan jami’an NDLEA na Lagos su tabbatar sun kakkabe jihar daga muggan ’yan kwaya da sauran masu tu’ammali da ita, kama daga sayarwa, safarar ta da jigilar ta.
Daga cikin dalilan da ya bayar na yawa da tumbatsar hada-hadar kwayoyi a Lagos, har da saboda yawan dimbin jama’ar da ke birnin, tashoshin jiragen ruwa biyu da ke Lagos, filayen jirage da kuma dimbin kantinan sayar da magungunan da ba su da rajista.
Daga nan ya kara da cewa akwai ‘kemis-kemis’ da sauran dakunan sayar da magunguna a cikin kasar nan har guda milyan daya da guda 58,000 a fadin kasar nan.
Ya ce a cikin su, 58,000 ne kadai ke da rajista, amma sauran milyan daya ba su rajista ko ta takardar tsire.
Duk da irin yawan da masu tu’ammali da kwayoyi ke cikin Lagos, hakan bai hana Marwa jinjina wa Kwamandan NDLEA na Jihar Lagos ba, Ralph Igwenagu.
Ya ce ba don kokarin da kwamandan da sauran zaratan jami’an sa ke yi ba, to da tuni masu tu’ammali da muggan kwayoyi a Legas sun wuce yawan da su ke da shi a yanzu.