Shugaban kwamitin dakile yaduwar cututtuka na majalisar dokokin jihar Kano Bashir Lawal ya bayyana cewa wasu mutum hudu sun mutu sannan likitoci na duba mutum 189 a asibiti a jihar a dalilin kwankwadar wani gurbataccen lemon kwalba.
Da yake bayyana haka a hira da yayi da manema labarai a garin Kano ranar Talata Lawal ya ce an samu aka si ne bayan mutanen sun kwankwadi wani lemon kwalba da ya lalace.
Ya ce wannan an samu labarin wannan matsala ne a kananan hukumomi 8.
Wadanda suka sha lemun sun fara ganin jiri, amai da gudawa da yin fitsari da jini.
A dalilin haka gwamnati ta aika wa hukumar NAFDAC sumfurin lemun kwalban da mutane suka sha domin gudanar da bincike.
Sakamakon gwajin da hukumar NAFDAC ta fitar ya nuna cewa lemun kwalban ya zama guba ne saboda an hada shi da kayan hadin da basu da inganci.
Hukumar ta kuma ce ta gano guban a cikin ruwan leda na sha da ake siyarwa a jihar.
Lawal ya ce gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin ganin an kawo karshen wannan matsala musamman a kananan hukumomin da matsalar ta bullo.
Bayan haka shugaban hukumar kula da ingancin abinci na jihar Baffa Babba-Da’agundi ya ce sun kama mutum hudu dake da hannu wajen saida wannan lemu sannnan sun gano wurin da ake ajiye lemun kwalban a karamar hukumar Minjibir.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar ta yi kira ga mutane da su rika kula da ingancin abincin da suke ci musamman yanzu da aka shiga yanayi na zafi.
Discussion about this post