Wadume, Gogarman mai garkuwa da mutane zai fara fafutikar kare kan sa a kotu

0

Sakamakon kammala gabatar da shaidun mutum shida da mai gabatar da kara ya kammala, shi kuma wanda ake kara, wato gogarman masu garkuwa da mutane, Wadume, zai fara kare kan sa daga tuhumar da ake yi masa a ranar 8 Ga Mayu.

Wanda ake zargin, wato Hamisu Bala, da aka fi sani da Wadume, tare da wadanda ake tuhumar sa tare za su fara kare kan su daga tuhumar garkuwa da mutane a ranar 8 Ga Mayu, a Babbar Kotun Tarayya a Abuja.

Cikin watan Yuni ne a ranar 8 Ga wata, 2020, Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da Wadume a Kotun Tarayya da ke Abuja, inda aka tuhume su da laifuka 13, wadanda su ka hada da ta’addanci, garkuwa da mutane, sai kuma wasu laifuka da dama.

Sauran wadanda ake tuhuma tare da Wadume sun hada da Sufeton ’Yan Sanda Aliyu Dadje, Auwalu Bala, Uba Bala, Bashir Waziri, Zubairu Abdullahi da kuma Tayyanu Abdul.

Yayin da aka ci gaba da sauraren karar a ranar Talata, jagoran lauyoyin da ke gabatar da kara, mai suna Shuaubu Labaran, ya kira mai bada shaida na shida, kuma wanda shi ne mai bada shaida na karshe, wani Sufeton ’Yan Sanda mai suna Ben Anthony.

Lauyan da ke cikin masu gabatar da kara main suna Yetunde Cole, ta shaida wa kotu cewa Anthony na cikin gugun jami’an ‘yan sandan da su ka kwato bindiga AK-47 daga hannun wani dan uwan Wadume mai suna Uba Bala, a garin Ibbi, Jihar Taraba.

Anthony dai ya bayar da dogon bayanin yadda su ka kama Bala ya kai su inda ya turbude bindigar a cikin wani kango.

Ya ce sun yi amfani a kwashe da magirbi sannan su ka ciro bindigar daga cikin ramin da aka gina aka binne ta.

Daga nan sai babban lauyan da ke jagorantar gungun lauyoyin da ke kare Wadume, mai suna Dikko Ishaku, a madadin sauran lauyoyin da ke kare shi,ya roki kotu ta aza ranar da za su fara Wadume.

Sai dai kuma lauyan wanda ake tuhuma na uku, mai suna Y. Dangana ya shaida wa Mai shari’a cewa wanda ya ke karewa din ba zai tsaya kare kan sa ba, amma ya na sanar da kotu cewa bai aikata abin da ake zargin sa ba.

Mai Shari’a Binta Nyako ta ce to duk wanda zai gabatar da uzirin ba zai tsaya bata lokacin kare kai ba, zai iya yi cikin kwanaki 21.

Daga nan an daga ci gaba da sauraren shari’a zuwa ranar 18 Ga Mayu, domin su Wadume su fara kare kan su.

An kama Wadume a ranar 6 Ga Augusta 2019. PREMIUM TIMES kuma ta buga labarin dambarwar da ta faru a wani kokarin tserewa da Wadume ya son yi daga hannun ‘yan sanda, wadanda daga bisani su ka kamo shi.

Ya tsere ne da taimakon sojoji wadanda suka kashe ’yan sanda uku kuma su ka ji wa biyar rauni a harin da su ka kai masu bayan sun kamo Wadume.

Share.

game da Author