JIDALIN KARIN ALBASHI: Kungiyoyin Kwadago sun yi barazanar hargitsa Najeriya

0

“Za mu sadaukar da jinainan mu wajen bijire wa duk wani tsarin gwamnati mai kuntatawa da nakasa talakawa…. Sannan mu yi zanga-zangar da za a ce ashe tarzomar #EndSARS wasan yara ce.”

Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Kasa a karkashin NLC, TUC da kuma NULGE, tare da sauran kunigiyoyi, sun gudanar da zanga-zangar kin amincewa a cire kudirin dokar mafi kankantar albashi daga Majalisar Tarayya.

Shugabannin Jihar Lagos na TUC da NLC sun bayyana cewa sun shirya idan ma yakin fito-na-fito za a yi, sun sadaukar da jinainan su.

Kuma sun ce za su yi gangamin da za su tsayar da komai cak a kasar nan, idan har Majalisar Tarayya ba ta janye shirin tsame kudirin dokar karin albashi daga Majalisar da ta ke shirin yi ba.

“A matsayin mu na Hadaddiyar Kungiyar Kwadago, mun shirya bijire wa wannan kudirin janye karin mafi kankantar albashi daga Majalisa. Kuma idan ta kama, za mu yi zanga-zangar da za mu tsayar da komai wuri daya cak a fadin kasar nan.

“Wannan ba kurari ko barazana ba ce, matsayar mu ce mu ka bayyana wa duk wani mai kunnen kashi ya kwana da sanin matakin da za mu dauka, kuma babu gudu ba ja-da-baya.”

Haka Shugaban Kungiyar Kwadago Reshen TUC na Jihar Lagos, Gbenga Ekundayo ya tabbatar.

Ekundayo ya ce tabbas kasar nan ta yi shirin fuskantar gagariminn yajin aikin da a tarihi ba a taba gani ba, idan har Majalisar Tarayya ba ja janye daga nufin ta ba.

Shugabar NLC Reshen Jihar Lagos, Funmi Sessi, ta bayyana cewa wani Sanata Mohammed Dati ne ya gabatar da kudirin neman a cire kudirin dokar mafi kankantar allbashi daga Majalisar Dattawa.

“Saboda haka, za mu sadaukar da komai domin mu ki amincewa da wannan karkataccen tunani na sa.” Inji Funmi.

“Kungiyoyin Kwadago sun saba yin surutai da hargowa da kwakwazo da bakin su. To amma daga wannan karon za su fara fitowa ya yi yaki kawai.

“Mu na wani irin zama da rayuwa a Najeriya, inda talauci da yunwa da fatara da rashin tsaro sun sa kowa ya fusata iyakar wuya.

“Shugabanni na wawure mana hakkin da ya kamata da wanda ya wajaba a ba mu. Su na wannan satar rashin-kunya a gaban idon mu. Su na facaka da almubazzaranci da dukiyar mu, tare da azurta kan su da ’ya’yayen su. To a yanzu kan mage ya waye. A shirye mu ke da mu yake su, mu fatattake su.”

An dai gudanar da wannan zanga-zanga a fadin kasar nan a ranar Laraba, inda Funmi ta ce idan aka yi wasa da hankalin ma’aikata da kuma rayuwar su ta hanyar watsar da batun karin albashi, to a yi shirin ganin gagarimar zanga-zangar da sai an ce ashe tarzomar #End SARS wasan yara ce.

Share.

game da Author