Kano ta karbi allurar rigakafin korona 209, 520

0

Yayin da yake karbar allurar rigakafin, a filin sauka da tashin jirage na malam Aminu Kano, Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Aminu Tsanyawa ya ce rigakafin kashi na farko zai fi mayar da hankali ne kan ma’aikatan lafiya.

Kwamishinan wanda ya wakilci gwamna Abdullahi Ganduje ya ce gwamnan ya karbi rigakafin kuma nan bada jimawa ba za’a yi masa allurar rigakafin.

A cewarsa, za su fi mayar da hankali wajen yiwa mutanen dake da matsalar rashin lafiya rigakafin yayin da kaso na hudu kuma za’ ayiwa kowa da kowa.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa kwamitin yaki da Korona zai tattauna yadda tsarin yin rigakafin zai kasance da kuma lokacin da za’a fara.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin wasu asibitoci har 509 da gwamnatin Kano ta kebe domin a rika yi wa mutane rigakafin Korona.

Jihar Jigawa

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru ya yi allurar rigakafin Korona a gidan gwamnatin jihar dake Dutse.

Allurar wadda daya daga cikin likitocin gidan gwamnatin ya tsirawa gwamnan allurar da misalin karfe 1: 45 na yau Laraba.

Gwaman ya kuma karbi shaidar yi masa allurar mintuna kadan da yi masa allurar.

Daga bisani Gwamnan ya shaidawa yan Jaridu cewa allurar rigakafin korona bata da illa saboda ta samu shaidar hukumar lafiya ta duniya.

Yace mataimakin sa Muhammad Namadi da wasu daga cikin kwamishoni suma anyi masu rigakafin ta korona.

Ya kuma cewa malaman addinai da ma’aikan lafiya a Jihar suna daya daga cikin wadanda za’a fara yayiwa allurar rigakafin.

Bayan haka Badaru ya hori ‘Yan Jigawa su amince ayi musu rigakafin, yana mai cewa sannu a hankali, allurar rigakafin zata iso lungu da sako na Jigawa.

Jihar Jigawa ta sami addadin allurar rigakafin korona 68,520 daga gwamnatin tarayya wanda yayi daidai da kashe daya na cikin yawan al’umma mai yawan mutum kimanin miliyan biyar.

Share.

game da Author