Sakamakon gwajin Korona da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na wannan mako ya nuna cewa mutum 2,382 suka kamu da cutar sannan mutum 47 suka mutu a sanadiyyar cutar daga ranar litinin zuwa Juma’a, 5 ga Maris.
An yi wa mutum 1,544,008 gwajin cutar a kasar nan. Daga ciki mutum 158,042 sun kamu.
Zuwa yanzu mutum 19,063 na killace a wuraren da ake kula da waɗanda suka kamu, an sallami mutum 137,025. Mutum 1,954 sun mutu.
Jihar Legas, Abuja, Filato, Kaduna, Oyo, Rivers, Edo, Ogun ne suka fi yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.
Zuwa yanzu yaduwar cutar ta fara raguwa haka kuma mutuwa daga cutar ya fara raguwa a kasan.
An fara yi wa jami’an lafiya allurar rigakafin korona a Abuja
Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA ta fara yi wa jami’an lafiya dake aiki a asibitin ƙasa a Abuja allurar rigakafin cutar korona ranar Juma’a.
Shugaban kwamitin PTF kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce gwamnati ta yi haka ne domin kare kiwon lafiyar jami’an lafiya ganin sune ke kula da marasa lafiya a asibitoci.
Wani likita mai suna Cyprian Ngong da wasu jami’an lafiya uku aka fara yi wa rigakafin Korona a kasar nan.
A ranar Talata ne rigakafin Korona miliyan 4 suka iso kasar nan.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan dakile yaɗuwar cutar Korona a Najeriya Boss Mustapha, ministan Lafiya, Osagie Ehinare, da wasu jami’an gwamnati ne suka tarbi isowar maganin daga kasar Indiya a filin jirgin dama na Abuja.
Tuni har an yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, da mataimakin sa, Yemi Osinbajo rigakafin cutar a fadar gwamnati ranar Asabar.
Discussion about this post