Yayin da tsohuwar matar Femi Fani-Kayode mai suna Precious Chikwendu ta garzaya kotu domin neman a ba ta hakkin kula da ’ya’yan su hudu, shi kuma kasagin, wanda ya taba yin Ministan Harkokin Sufurin jirage, ya bayyana cewa Precious na kwantaccen da tabin-hankalin da ke tashi a duk lokcin da ta ke cikin fushi.
Sannan kuma ya ce tun da ya aure t bai taba dirka mata dukan tsiya kamar yadda ta rika ikirari ba.
“Wannan matar ai tantagaryar makaryaciya ce. Kuma zan tabbatar da haka a kotu. Bai ma kamata a ce ta zama uwar wani ba. Matar da ke nuna wa kananan yara kuma ‘ya’yan ta keta, sannan ba ta taba kula da su ba, ta yaya za a ce a ba ta yaran ta kire su?” Inji Femi Kayode, ta bakin jami’in yada labaran sa, Oladimeji Olaiya.
“Mun hakkake cewa rayuwar yaran za ta kasance cikin hatsari idan su na tare da ita. Kuma za mu tabbatar da haka a kotu.
“Shi kuma Fani-Kayode ko sau daya bai taba nuna wata alamar yaran na cikin hatsari a hannun sa ba. Ya samar masu masu kula da su, har masu raino su 12 da nas-nas wadanda ke yin bakin kokarin su, har a lokacin da ita mahaifiyar ta su ta na gida na, ta san da haka.”
Precious dai ta zargi Fani-Kayode da yawan jibgar ta, har lokacin da ta ke dauke da juna-biyu.
Precious, wadda ta taba zama sarauniyar kyau, ta na neman kotu ta karbo yaran da ta haifa su hudu tare Fani-Kayode a damka mata hakkin mallakar kula da su.
Ta ce tsawon watanni a dama kenan ya hana ta ganin yaran su hudu.
Dalili kenan ta ke neman kotu ta maida su a hannun ta, kuma ta nemi kotu ta tilasta shi ya rika biyan ta naira milyan 3.5 a kowane wata, domin daukar dawainiyar yaran a hannun ta.
An dai bayyana tsinkewar igiyar aure a tsakanin su cikin watan Satumba, 2020.
Sun yi aure cikin 2014, inda tsawon zaman su sun haifi yara hudu, wadanda na farko namiji da kuma wasu ‘yan-uku duk maza da aka haifa shekaru biyu da su ka gabata.
An haifi Precious cikin 1989, kuma ta wakilci Najeriya a Gasar Sarainiyar Kyau ta Majalisar Dinkin Duniya, cikin 2014.