Kungiyar ma’aikatan majalisun dokokin jihohin Najeriya (PASAN) reshin Jihar Jigawa ta garkame majalisar dokokin Jihar domin kin cika alkawarin da gwamna Muhammad Badaru yayi na basu damar cin gashin kan su a majalisar.
Daruruwan ma’aikatan cikin zanga-zangar lumana sun rufe kofar shiga majalisar, sannan sun haramtawa yan majalisun da sauran jama’a shiga harabar ginin majalisar.
Masu zanga-zangan sun bayyana cewa ba za su yadda wani ya shiga harabar majalisar ba sai gwamnati ta biya musu bukatun su.
Sun ce Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da dokar basu yancin tafiyar da al’amurorin su ba tare da ana yi wa musu katsalandan ta kowani yanayi ba amma kuma gwamna Badaru da wasu takwarorinsa sun yi wa wannan umarni kunnen uwar shegu.
Shugaban kungiyar reshin Jihar Jigawa Umar Kazaure, yace sun fara yajin aikin ne da rufe majalisar bayan sun bada wa’adi na kwanaki 21 domin jan hankalin gwamnati kan bukatun nasu amma sun ki waiwayan su.
Kazaure yace mambobin kungiyar sunyi shekara biyu suna zaman hakuri duk da cewa shugaba Buhari ya amince da bukatun nasu amma gwamnoni sunki aiwatarwa.
Jami’in ya kara da cewa yajin aikin na kasa ne baki daya ba iya jihar Jigawa bane, kuma zasu ci gaba dayi har sai an biya masu bukatunsu na cin gashin kai.