Buhari na kokarin samar wa masu hakar ma’adinan Najeriya mafita daga matsalolin tsaron da su ka addabe su

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tabbas akwai kalubale daban-daban a kasar nan, kuma ana aiki ba dare ba rana domin ganin an kawar da wadannan kalubale, musamman wadanda su ka shafi matsalar tsaro.

Ya yi wannan bayani wurin Taro na 56 na Kungiyar Masana Albarkatun Kasa da Mahaka Ma’adinai ta Najeriya (NMGS), wanda aka kammala a Ibadan.

Mahalarta taron da dama su ma wannan damuwar su ka nuna tare da neman yadda za a shawo kan kalubalen domin a saukaka harkokin hakar ma’adinai a kasar nan.

Buhari ya nuna masu damuwar yadda matsalar tsaro ta kori masu sana’ar ma’adinai daga wuraren aikin su.

Wannan matsala da ta shafi masu hakar ma’adinai kuwa injiBuhari, ta shafi gwamnati, domin gwamnati ba ta samunkudin shiga dga masu aikin ma’adinan idan su na fama da matsalar tsaron da ke hana su gudanar da ayyukan su.

“Gwamnati ta lura da cewa ayyukan masu hakar ma’adinai duk a cikin dazuka ake gudanar da su. Sannan abin takaici kuma mahara da sauran ’yan bindiga su ma a cikin dajin su ke ta’addancin su.

“Su na takura wa masu aikin hakar ma’adinai ta hanyar kwasar dukiyar da su ke amfani da ita su na kara wa kan su karfi.

“Wannan ne dalilin da ya sa kwanan nan mu ka hana duk wani ayyukan hakar ma’adinai a Jihar Zamfara, inda ‘yan bindiga ke ci gaba da tashe-tashen hankula.”

Daga nan sai Shugaba Buhari ya nemi hakin kai da hadin guiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ma’adinai, gwamnatocin johohi da dukkan bangarorin jami’an tsaro, domin a tabbatar da tsaron masu hakar ma’adinai da yankunan da ma’adinan su ke.

Buhari ya ce tabbas “duk al’ummar da matsalar tsaro ya dabaibaye, to zai yi wahala ta samu wani ci gaba na a zo a gani.”

Shi ma Babban Daraktan Ofishin Kula da Harkokin Ma’adinai (MCO), Simon Nkom, bayyana cewa Kungiyar Masana Albarkatun Kasa da Masu Hakar Ma’adinai ta rasa rayukan mambobin ta da abokan harkar ta a hare-haren ta’addancin Arewa maso Gabas a lokacin gudanar da ayyukan su.

“Ayyukan da mambobin mu ke yi duk a cikin surkukin dazuka su ke gudanar da su. A matsayin mu na masu bayar da gudummawa wajen bunkasa arzkin kasa, za mu amfani da wannan raro domin mu fito da matsalollin da mu ke fuksanta tare da kawo shawarwarin hanyoyin da za a magance su.” Inji shi.

Share.

game da Author