Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tafiyar-hawainiya da tafiyar-kura, a cikin yanayin karin yawaitar rashin aiki da tsadar rayuwa, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dukufa wajen laluben mafita, ta hanyar yi wa wasu tsare-tsaren hada-hadar kudade garambawul.
Sanarwar wannan mataki da za a yi sanarwar gaggawar dauka a yammacin ranar Talata, ta fito ne daga bakin Gwamnan Bankin, Godwin Emefiele a ranar Talata.
A yau Talata ce Gwamnan zai yi ganawa da manema labarai, misalign karfe 2:15 na yamma, inda zai bayyana sanarwar matakan da CBN zai dauka.
Masana sirrin irin ruguguwar da tattalin arzikin Najeriya ya rufta na ganin cewa kwamiti zai duba kokarin da Najeriya ke yi wajen gudanar da allurar rigakafin korona domin dakile cutar, matsin tsadar kaya da rashin aikin yi ga dimbin jama’a da kuma halin da kasuwa ke ciki, musamman irin yadda ta ke shafar masu samun kudin shigar da ba su gaba ba su baya, kamar ’yan albashi da sauran su.
‘Halin Damuwar Da Ake Ciki’:
Tattalin arzikin Najeriya ya fada halin kaka-ni-ka-yi, inda ba ya gaba sai dai baya, ga dimbin bashi ya cika ruwan cikin gwamnatin kasar, ga rashin aikin yi da ke karuwa, ga tsadar kayan abinci, ga kuma karancin samun kudin shiga ga dimbin jama’a. Sannan kuma kudin ba su da albarka kamar da.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda malijin tsadar rayuwa ke kara hauhawa a Najeriya, inda kayan abinci ya yi tsadar da shekaru 13 baya ba su gigita ’yan Najeiya irin haka ba.