Shugaba Muhammadu Buhari yayi kiran cewa ya zama wajibi a yi wa Kungiyar Kasashen Afrika kwaskwarima da garambawul.
Buhari ya ce hakan ya zama wajibi domin kungiyar ta rika cimma dukkan kudirorin da ta sa gaba da nufin ganin ta cimma.
Ya matsawar dai kungiyar ba ta iya tabuka komai wajen cimma kudirorin ta, to za ta zama tsohon yayi kenan.
Ya gode wa Shugaba Paul Kigame na Rwanda a kan takardar neman mafita ga Kungiyar Kasashen Afrika da ya gabatar a wurin taro.
A taron kungiyar wanda aka yi karo na 34, amma daga gida, Buhari ya bayyana cewa, “Shugabannin Afrika kakaf na sane da cewa yanzu a duniya ta ci gaba, don haka Kungiyar Kasashen Afrika ba za ta zama wata mai wani tasiri ba, har sai an yi mata garambawul din da za ta iya cimma kudirorin da ta dauki himmar kaiwa.
“Najeriya na yin kira da babbar murya a gaggauta samar da canji, garambawul da kwaskwarima ga Kungiyar Kasashen Afrika, ta yadda kungiyar za ta iya gudanarwa da aiwatar a ayyukan da su ka wajaba da wadanda su ka kamace ta.”
Buhari ya kuma gode da goyon bayan da Shugabannin Kasashen Afrika su na bayar ga Najeriya har aka zabi Bankole Adeoye matsayin Kwamishinan Harkokin Siyasa, Zaman Laiya da Tsaro na Kungiyar Kasashen Afrika.
A karshe ya kuma gode wa sauran zababbun mambobin kungiyar na 2021, da suka hada da Shugaba Moussa Faki Mahamat daga Chadi da kuma Mataimakin Shugaba, Monique Nsanzabagwanwa daga Rwanda.