Ganduje ya amince a gwabza mukabala tsakanin malaman da ke adawa da Sheikh AbdulJabbar da shehin a Kano

0

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya amince a gwabza mukabala tsakanin duka malaman Kano da ke jayayya da Sheikh AbdulJabbar Nasir Kabara da su a bainar jama’ a a Kano.

Gwamna Ganduje ya ce duk wani malami da ke kalubalantar karantarwar Sheikh Abduljabbar ya je ya shirya a kowacce darika yake, Sunna, Salaf, Tijjaniyya, Kadiriyya, shiia da sauransu nan da makonni biyu za a goge raini a Kano.

Sannan kuma ya ce gwam ati za ta samar da wajen da za a gwabza da tsaro.

Gwamnatin jihar ta. E yin haka shine zai warware duk wata cece-kuce da ake ta yi tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman kasar nan.

Idan ba a manta ba gwamnatin Kano ta dakatar da karatun da sheikh Abduljabbar yake yi a Kano cewa kalaman da yake furtawa kan Annabi SAW da sauran sahabai sabo ne karara.

Hakan yasa gwambati ta dakatar da shi sannan har rusa wata makarantar sa aka yi bayan zagaye gidan sa da jami’an tsaro.

Gwamnatin Kano kamar yadda Daily Nigerian ta buga, za ta shirya wannan mukabala sannan kuma za a yada shi a nuna a duka kafafen yada labarai na gida da kasashen waje.

Share.

game da Author