Fadar Shugaban Kasa ta soki jam’iyyar PDP saboda ta yi kiran Kotun Duniya ta hukunta Manyan Hafsoshin Sojan Najeriya hudu da su ka yi ritaya makonni biyu da su ka gabata.
Fadar ta Buhari ta bayyana nadin da aka yi wa su Janar Buratai na jakadun Najeriya, cewa wata lada ce aka biya su ta aiki tukuru da su ka sadaukar da kawunan su wajen bauta wa kasar su.
Wannan bayani na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Fadar ta bayyana cewa ko sarkin mahassada ya san cewa su Buratai sun yi wa kasar nan kokari bakin iyawar su.
Shehu ya kara da cewa shirme ne PDP ke yi cewa wai a gurfanar da su Buratai.
Haka kuma ya bayyana cewa abin dariya ma ganin yadda wasu kafafen yada labarai su ka cika kasar nan da labarai cewa an nada su Buratai ne mukaman jakadu domin a kange su daga tuhumar Kotun ICC ta duniya.
Shehu ya ci gaba da kare su Buratai, ya na bayyana irin kokarin da su ka yi wajen samar da tsaro a kasar nan, musamman a yaki a Boko Haram.
Daga nan kuma ya tunatar da PDP irin barnar da sojoji su ka yi a zamanin mulkin PDP, musamman a Zaki Biam da Odi.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda PDP da wasu lauyoyi su ka bayyana cewa Buhari ya nada su Buratai jakadu ne don kange su daga binciken Kotun Duniya.
Wasu lauyoyi sun bayyana kwararan dalilai biyar da su ka su ne dalilin da ya sa Shugaba Muhamadu Buhari ya yi gaggawar nada Tsoin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya ya nada su jakadu na kasashe baban-daban.
Lauyoyin sun ce an nada su Laftanar Janar Tukur Buratai mukaman jakadu ne don kada Kotun Kasa-da-kasa ta Duniya (ICC), ta damke su ta tuhume su da laifukan cin zarafin jama’a da kashe-kashen fararen hula.
Yarjejeniyar Diflomasiyyar Duniya ta 29 ta Taron Vienna Convention dai ta kange tare da haramta kamawa ko tuhumar duk wani jakadan wata kasa a tsakanin kasashen duniya, da nufin tuhumar sa da laifin cin zarafin fararen hula.
Wannan ya sa mutane da dama na ganin cewa Buhari ya yi gaggawar nada su Buratai mukamin jakadun ne don kada a tuhumi zargin kashe-kashen da su ka yi kan talakawa a karkashin mulkin sa.
Dama kuma tun a ranar da su ka sauka jama’a ke ta kiraye-kirayen a gurfanar da su a kotun hukunta laifukan cin zarafin jama’a ta duniya.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Tsoffin Hafsoshin Tsaron Najeriya gata, ya nada su jakadun kasashe daban-daban, mako daya bayan ritayar su.
Wannan gaggawar nadi ta jefa zargi a zukatan jama’a da dama, musamman lauyoyi da a yanzu ke cewa an nada su don a kare su daga tuhumar kotun binciken cin zarafin fararen hula.
Wasu zarge-zargen da ake yi masu, musamman Tukur Buratai, ya hada da kisan-kiyashin ‘yan Shi’a da aka yi a Zariya, cikin watan Disamba, 2015, kisan ‘yan kungiyar IPOB da kuma kisan masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Lagos, cikin 2020.
Gabriel Olonisakin; Tukur Buratai; Ibok Ibas da Abubakar Sadique ne aka nada mukaman jakadun bayan ritayar su.
PDP Ta Nemi ICC da INTERPOL Su Damke Su Buratai A Hukunta Su:
Dama kuma jim kadan bayan ritayar su, jam’iyyar PDP ta yi kira ga Kotun Duniya (ICC) da INTERPOL su gaggauta kama su Buratai su hukunta.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Olagbondiyan ya fitar, ya bayyana cewa su Buratai sun aikata kisan rashin imani da kisan kiyashi a kan araren hula.
Mun Samu Bayanan Da Za Mu Iya Bincikar Buratai –ICC
Cikin shekarar da ta gabata ne Babban Mai Gabatar da Kara na Kotun ICC, Fatou Bensouda, ya yi bayanin cewa sun samu gamsassun bayanan da za su iya bincikar su Buratai kan zargin aikata laifuka a yakin ta’addanci da Boko Haram da Sojojin Najeriya ke kan yi.
Sai dai tun a lokacin Buratai ya ce duk surutai ne, amma lamarin ba ya tsorata shi ko firgita shi.
Sulken Kariyar Bincike Da Buhari Ya Lullube Su Burutai:
Yarjejeniyar Vienna Convention Sashe na 29:
“Duk wani jakadan wata kasa ya haramta wata kasa ta kama shi domin bincike ko gurfanarwa kotu, duk irin laifin da ya aikata. Sulken kariya gare su, ba za a kama su ko hukunta su ba.
“Kada kasar da su ke a zaune ta tura jami’ai a binciki gidajen su ko kwace wasu kadarori ko kayayyakin su.
Afam Osigwe da Inibehe Effiong da wasu lauyoyi da dama, sun cika da mamakin wannan gagarimin laifi da Gwamnatin Buhari ke kokarin binnewa.
Sun yi kira kada Majalisar Dattawa ta amince da nadin mukaman jakadun da Buhari ya nada su Buratai.