Ayyukan da Ngozi Okonjo-Iweala za ta yi a WTO

0

‘Yar Najeriya ta farko kuma ta farko a bakar fata sannan ta farko a Afrika wadda aka nada Shugabar Kungiyar Hada-hadar Kasuwanci ta Duniya (WTO), wato Ngozi Okonjo-Iweala za ta gudanar da gagarimin ayyuka ne a cibiyar da su ka shafi harkokin tattalin arzikin kasashen duniya.

Za ta fara aikin shekara biyar daga ranar 1 Ga Maris, 2021. Sai dai mutane da dama ba su san yadda WTO ke gudanar da ayyukan ta ba. Kuma ba a san irin gudummawar rawar da ta ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki ba.

WTO: ita dai wannan kungiya ta kunshi dukkan wasu harkokin hada-hadar kasuwanci da cinikayya tsakanin kasashen duniya.

An kafa wannan kungiya ka’in-da-na’in a ranar 1 Ga Janairu, 1995, amma dai tun asali za ta kai shekaru 50 da fara bijiro da ita.

Babban aikin ta shi ne ta tabbatar an gudanar da huldar kasuwacnci da cinikakkaya tsakanin kasashen a bayyane, yadda hada-hadar za ta amfani kowa.

WTO aikin ta ne kula da kuma sa-ido kan duk wata yarjejeniyar cinikayya da kasashe su ka kulla. Tare kuma da tabbatar da cewa kowane bangare ya cika alkawari da kuma bin ka’idar rubutacciyar yarjejeniyar.

Sannan kuma aikin WTO ne ta sasanta sabanin da ka iya tashi a batun cnikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma za ta iya shiga tsakani wajen kulla wata yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kasashe wajen zama tsani da sauran su.

Ta na kuma taimaka wa matalautan kasashe da kasashe masu tasowa da sauran kasashe masu karancin nauyin aljihu wajen tabbatar da bada horo ga jami’an su, domin domin samun shiga harkokin hada-hadar cinikayya ta yadda za a rika damawa ana shanyewa tare da su a duniya.

Domin samun daidaito da bunkasar tattain arziki a duniya, WTO na hada kai da manyan cibiyoyin hadar-hadar kudade na duniya, irin su IMF.

WTO na samun kudaden shigar da ta ke kasaftawa ta hanyar karo-karon da kasashen da ke cikin kungiyar ke bayarwa.

WTO na da sauran kananan hanyoyin samun kudaden shiga. Sannan kuma kungiya ce mai mambobi 160 na kasashen duniya daban-daban.

Share.

game da Author