Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya hori ‘yan Najeriya da su rika tunkarar ‘yan bindiga idan tuka afka musu.
Magashi ya bayyana wa manema labarai cewa dole fa sai ‘yan Najeriya sun jajirce, sun zama jarumai a koda yaushe idan har ana son a kawao karshen hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.
” Wai shin sojoji ne kawai samar da tsaro ya rataya a kan su? tabbatar da tsaro a kasa na kowa da kowa ne. Dole a maida hankali matuka a tsaya cikin shiri a koda yaushe.
” Kada kuma a taro a zama daya mana wato matsorata. Kada ku rika arcewa idan mahara suka diran muku, tsaya zaku yi a fafata, a yi arangama ba ku tsorata ba ku rika arcewa.
” Locatin da muke samari ba mu gujewa irin haka tsaya kem muke yi mu tunkari irin wadannan mutane ayi ta agama kawai.
Wadannan kalamai na Bashir Magashi ya tada wa ‘yan Najerirya hankali da bacin rai.
” Wadannan kalamai ba su dadin ji ko kadan a ce wai ministan tsaron kasa ne zai rika yi wa mutanen sa irin kalami kamar haka. Ya nufin kowa ya je ya siya makami ke nan a kasar nan domin ya karae kan sa. Bai kamata a ce wai shugaba ne ki bada irin wannan shawara ba. Inji wani mai yin sharhia yanar gizo.