KANO: Yadda miji ya kama Kwamandan Hisbah da matar sa a Otal

0

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano sun damke wani Kwamandan Hisbah mai suna Sani Nasii Uba Remo, tare da wata matar aure a cikin otal, a Kano.

Bayanan da suka fito tun a ranar 16 Ga Fabrairu, sun tabbatar da cewa an damke Sani a cikin dakin otal din tare da matar, wadda aka tabbatar matar aure ce, a unguwar Sabongari.

Mijin matar ne ya kai korafi ga ‘yan sanda, kuma aka dana masa tarko aka kama su a cikin dakin.

Sabongari, unguwar da aka kama shi, ita ce matattarar karuwar da shaye-shaye da auran ayyukan masha’a da aka kafa Hukumar Hisbah domin ta yi aikin hanawa.

Shi kan sa Kwamndan Hisbah din ya taba rike shugabancin bangaren Hisbah na zaratan kamen karuwai da kangararrun ‘yan mata a cikin Sabongari.

Hukumar Hisbah ta Kano ta tabbatar da kama kwamandan na ta a Nomansland, wani bangare na Sabongari da masu aikata masha’a da sharholiya ke zuwa su na holewa.

Bayan kama shi da jami’an tsaro su ka yi, an kulle shi a ofishin ‘yan sanda na Nomansland da ke cikin Sabongari, Kano.

Babban abin takaici shi ne mijin matar ne ya yi jagoran ‘yan sanda aka kamo Sani Kwamandan Hisbah tare da matar aure a cikinn otal.

Yayin da Sahelian Times ta tabbatar da cewa wani Mataimakin Kwamandan Hisbah ne ya je yi belin Kwamandan Hisbah Sani daga wurin ‘yan sanda, ita kuma Daily Trust ta ranar 18 Ga Fabrairu ta bayyana cewa kwamandan ya shaida cewa ba badala ya je yi da matar ba.

Ya ce wata ‘yar uwar sa ce, amma ta samu matsala da mijin ta, shi ne a jiye ta otal kafin a samu sasanta ta da mjin na ta.

Babban Kwamanda Janar na Hisbah ta Kano baki daya, Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina, ya tabbatar da mummunan lamarin, kuma ya kara da cewa yanzu Sani ya na hunnun su, su kuma sun dukufa bincike.

Ya ce ya kafa kwamitin da zai kai masa rahoton binciken lamarin cikin kwanaki uku.

A lokacin da aka kama Sani, shi ne Kwamandan Kamen Almajirai masu bara kan titi.

Kafin nan kuma shi ne Kwamandan Kamen Karuwai da Kangararrun ’Yan Mata a Sabongari, Kano.

Share.

game da Author