Yadda ’yan bindiga su ka kashe Shugaban Karamar Hukumar da su ka yi garkuwa da shi a Taraba

0

Masu garkuwa sun kashe Shugaban Karamar Hukumar Ardo-Kola ta Jihar Tabara, bayan sun yi garkuwa da shi a ranar Lahadi.

An kashe Salihu Dogo bayan an arce da shi, a wani hari da aka tabbatar da cewa masu garkuwa ne su ka tafi da shi.

An tabbatar cewa masu garkuwa sun kira wani jami’in karamar hukumar su ka shaida masa cewa sun kashe shugaban karamar hukumar, tare da kiran su su je su dauki gawar sa.

Sai dai kuma wasu mazauna yankin na zargin cewa sojojin haya ne aka tura domin kawai su kashe shi, amma ba masu garkuwa ba ne.

“Bayan sun kira cewa sun kashe shi, a je a dauki gawar sa, sai jama’a su ka shiga daji neman gawar sa, kuma aka gano gawar.

Majiya ta ce zuwa lokacin da ake hada wannan labari har an kai gawar sa cikin garin gari, kuma ta na asibiti.

Kisan na sa ya faru n bayan da wasu ‘yan bindiga su ka shiga gidan sa da karfin tsiya a Sabon Garin Jalingo wajen karfe 1 na dare, su ka tafi da shi.

Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sandan Jihar David Misal, ya tabbatarc da cewa har ma sun kama wanda su ke zargi da laifin kisan.

“Yanzu haka gawar mamacin na asibiti ajiye tukunna. Kuma mun kama mutum daya da ake zargi.”

Share.

game da Author