A cikin watan Nuwamba dai malejin kunci da tsadar rayuwa a Najeriya ya karu da kashi 14.89, inda tsadar kayan abinci ya kai kashi 18.30.
Wani rahoto ya bayyana wasu dalilan da ke kara wa rayuwa tsada a kasar nan, musamman bangaren hauhawar farashin kayan abinci.
Dalilan dai sun hada da rashin kyanb titinan da ake daukar kayan abincin daga garuruwa zuwa wasu garuruwa. Akwai kuma haraji daban-daban daga na Kananan Hukumomi, Jihohi da kuma na Gwamnatin Tarayya duk a na tare hanyoyi ana karba daga hannun masu kayan abinci, akwai rashin ingantaccen wurin adana kayan abinci da kuma irin tsananin takurawar da jami’an tsaro ke wa masu safarar kayan abinci su na karbar cin hanci da salon maula kala daban-daban a hannnun su.
Rahoton da SBM Intel ya buga a ranar Talata ya maida hankali ne wajen gudanar da binciken kwakwaf a kan lamarin, ta yadda za a bi hanyoyi daban-daban wajen magance wadannan manyan matsaloli.
Rahoton ya maida hankali ne wajen samun bayanai daga manoma da kuma masu safarar kayan abinci daga garuruwa daban-daban a jihohi bakwai da su ka hada da Lagos, Ogun, Oyo, Nasarawa, Osun, Katsina da kuma Benue.
Har yau rahoton ya nuna damuwa a kan yadda wasu kayan gona ke saurin lalacewa saboda babu hanyoyin adana su zuwa wani tsawon lokaci. Wato tilas za a sayar da su a lokacin da aka debe su daga gonaki ko lambuna ko wasu kasuwanni.
Binciken da SBM Intel ya yi ya nuna kusan kashi 47 bisa 100 na manoman da aka ji ta bakin su, ba su da hanya ko wadatar dabarar adana kayan gona masu saurin lalacewa.
Wasu kashi 5.33 na manoma da masu safarar kayan kuma sun bayyana cewa matsalar rashin kyan hanya ne babbar matsalar da ta fi damun su wajen safarar kayan abinci.
Kashi 25 bisa 100 sun ce akwai matsallar yawan haraji barkatai ko a kan titi ko a kasuwanni.
Sai kuma kashi 21.7 su ka ce abin da ke damun su shi ne akwai yawan gallazawar da jami’an tsaro ke yi masu ta hanyar tare su su na karbar kudade a hannu su.
Sun ce rahin kyawon hanyoyi na kawo cikas ta hanyoyi da yawa ga kayan abinci.
Yayin da ake kaurace wa wasu garuruwan saboda matsalar rashin kyan hanya, sau da yawa kuma motocin daukar kayan abinci kan bugi ramu su fadi, kayan abincin su lalace a kan hanya.
A kan haka ne SBM Intel ke ganin cewa samun tsarin safarar kayan abinci ta hanyar zirga-zirgar sufurin jiragen kasa zai rage wannan matsala matuka, kuma za ta rage hauhawar farashin kayan bainci.
“Samun kyakkyawan tsaro abu ne muhimmin kwarai, sai kuma samun hanyar shiga wuraren dauko kayan abinci masu kyau tare kuma da tsarin noman rani mai inganci.”
Sauran ababen da ake bukata sun hada da kudade da wurin adana kayan abinci da sauran su.
“Masu safarar kayan abinci na bukatar samun hanyoyin noma masu kyau da kuma rage masu dan karen haraji daban-daban da ake tatsa a kullum a hannun su. Sai kuma matsalar yadda jami’an tsaro ke takura masu su ka karbar kudade a hannun su.”
SBM Intel ya ce a halin yanzu idan aka ta kai ba a ta kaya. Wato an tashi daga batun samar da wadataccen abinci, an koma wajen kokarin samar da ingantaccen tsaro ga harkar samar da abinci.”
Ya ce wannan tsari na farko ne ya haifar da tsadar kayan abinci a kasar nan.
“A irin wannan yanayi, ‘yan Najeriya ba su damu da batun samar da wadataccen abinci ba, saboda tsadar sa da kuma rashin tabbas a matsalar tsaron abinci. Kowa kawai jira ya ke ko ma daga ina abinci ya fito, kawai ya samu a saka a bakin salati.” Inji rahoton.