Zuwa yanzu dai ta-kacame da rudani da maganganu bayan da sojoji su ka bayyana kama wasu Fulani makiyaya da sojojin su ka ce an kama su ne yayin da su ke shirin kai harin ramuwar gayyar kisan da dakarun Amotekun dake aiki a jihohin Yarbawasu ka yi wa wasu Fulani a jihar Oyo.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an kama Fulanin ne ranar Lahadi a wani farmaki da sojoji su ka kai a Tapa/Igangan, yankin cikin Karamar Hukumar Ibarapa ta Arewa, a Jihar Oyo.
Majiyar cikin sojoji ta bayyana wa wakilin mu cewa makiyayan sun yi yunkurin kai hari na ramuwar gayya ne domin rama kisan wasu ‘yan uwan su da jami’an tsaro a Amotekun su ka yi masu ranar Asabar da ta gabata.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda dakarun Amotekun suka kashe wasu makiyaya uku a jihar Oyo.
Sai dai Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Oyo ya bayyana cewa ana tsare da makiyayan su 47 a ofishin CID da ke Iyaganku, Ibadan.
“Fulanin sun shaida mana cewa sojoji sun kama su ne a lokacin da su ke kokarin farautar wasu masu garkuwa, wadanda su ka yi garkuwa da wasu ‘yan uwan su domin a ba su kudin fansa.”
Shi kuma Shugaban Miyetti Allah na Jihar Oyo, Ibrahim Jiji, ya bayyana cewa Fulani makiyaya 47 da aka kama a jihar Oyo, ‘yan bijilante ne da ke sintiri a yankin Ibarapa.
“Wadanda sojoji su ka ba fa masu laifi ba ne. Su ne ke korar mana masu laifi su na yi mana sintiri. Kuma su na da rajista da jami’an yan sanda su na aiki tare da ma sauran jami’an tsaro.”
Ya ce wadanda aka kama din su na yi wa jihar Oyo amfani shekaru da dama. Amma ba masu laifi ba ne.
“Idan barawo barawo ne, to a kira shi barawo kawai. A daina yi wa Fulani jam’u, ana cewa duk barayi ne.”
Ya bayyana cewa tun farko shi ya sa su ka so a saka Fulani cikin tsaron Amotekun, saboda bambancin yare.