TSIGE SU BURATAI: ‘Koke-koken jama’ a 10 da suka sa aka yi fatali da Hafsoshin Tsaron Kasa’

0

A Yammacin Talatar nan ‘yan Najeriya sun cika da mamakin sauke Hafsoshin Tsaron Kasa hudu na Sojojin Kasa, na Ruwa, na Sama da Babban Hafsan Tsaro da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Sai dai kuma tun tuni ake ta roko da kiraye-kiraye ga Buhari ya tsige su, amma ya na kauda kai daga cire su din.

Masu sharhi na ganin tura-ta-kai-bango Buhari ya gaji da ji da ganin yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a karkashin manyan sojojin, har yau sun kasa shawo kan lamarin.

Ana hasashen wasu dalilai ne su ka sa Buhari ya hakura da su Laftanar Janar Tukur Buratai, ya maye gurbin su da sabbi.

1. Kasa shawo kan Boko Haram:

Ganin yadda Buhari ya rika cika-baki kafin ya hau mulki a kan matsalar tsaro, an yi tunanin cikin watanni shida na farkon mulkin sa zai iya magance matsalar Boko Haram.

Duk da an samu nasarar tare Boko Haram daga kai hare-hare sauran sassan kasa, amma har yanzu sun yi kaka-gida a jihohin Barno, Yobe, Adamawa da kuma kan iyakokin Najeriya da Nijar, Kamaru da Chadi.

Yawan hare-haren da su ke kai wa sojoji da kisan sojojin kan su na karuwa. Sannan kuma yaki da Boko Haram ya kara muni sosai, har ta kai ga an kara da sojojin sama da na ruwa a zamanin mulkin Buhari.

2. Kwararowar Kungiyar ISWAP cikin Najeriya, ya kara munantawa da tsananta yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas a karkashin mulkin Buhari.

Boko Haram sun shafe sama da shekaru biyu su ke fara kai wa sojoji hari, maimakon a ce sojojin ne ka fafarar su a sansannonin su.

3. An yi asarar sojoji masu dimbin yawa tsawon shekaru biyar ko shida na mulkin Buhari, kuma an yi asarar manyan kayan yaki sosai a hannun Boko Haram.

4. Har yanzu ana ci gaba da asarar dubban rayuka. Kuma a kullum Boko Haram sai sake salon kai hare-hare su ke yi, amma an kasa magance matsalar.

5. Shirin yi wa Boko Haram afuwa ana koya masu sana’o’i, bai yi wani tasiri ba, domin har yau babu alamun karewar ‘yan Boko Haram, sai ma karuwa da su ke yi, kuma sun ki ajiye makaman su.

6. Allah kadai ya san iyakar makudan kudaden da aka narkar da sunan kudin aikin tsaron kasa, amma kuma har yau sai kara afkawa cikin masifa ake yi a fadin kasar nan.

7. Furucin da Buratai ya yi watanni biyu da su ka gabata, ya sanyaya kugawun ‘yan Najeriya, inda ya ce mai yiwuwa a iya kai nan da shekaru 20 masu zuwa ba a magance Boko Haram ba.

Hakan na nuni da cewa nan da shekaru 20 kenan ba a san iyakar rayukan da Boko Haram za su kara kashewa ba. Kuma ba a san iyakar asarar makudan kudade, rayukan farar hula da rayukan sojojin da za a kara kashewa ba.

8. Mamayar da ‘yan bindiga su ka yi wa Yankin Arewa maso Yamma, da ya hada da jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto Kaduna ya zame wa sojojin Najeriya alakakai. Ta kai har jihar Katsina, mahaifar Shugaba Muhammadu ta fi sauran jihohin tashe-tashen hankula, garkuwa, banka wa kauyuka wuta, karbar makudan kudaden diyya da sauran ta’addanci.

Kullum abu ya ki ci ya ki cinyewa. Ana asarar rayuka, mazauna kauyuka sun kasa noma, sai gudun hijira ake yi.

Wannan bala’i ya yi katutu a Tsakiyar Najeriya, musamman a jihohin Neja da Kogi da Kudancin Kaduna.

9. Alamomi sai kara fitowa su ke yi cewa shugabancin manyan hafaoshin da aka sallama ba shi da tasirin kawo karshen kashe-kashen da ake yi nan gaba da wuri, ko kuma can gaba cikin shekaru masu zuwa.

10. Titin Abuja zuwa Kaduna mai nisan kilomita 167 daga Zuba zuwa Kaduna, ya gagari jami’an tsaron Najeriya hana ‘yan bindiga cin kasuwa a duk lokacin da su ke so. Ta kai a yanzu had da jiragen yaki a ke kai wa ‘yan bindiga farmaki a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wadannan dalilai da wasu masu yawa da ba a lissafa ba, sun nuna gazawar manyan hafsoshin Najeriya hudu a aka sauke wajen iya kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, musamman a Arewa, inda yankin ke neman komawa wata Daular Mulkin ‘Yan Bindiga.

Share.

game da Author