Mawakin nan dan Kano mai suna Yahaya Sharif-Aminu, wanda aka zarga da yin ridda, amma kotu ta sallame shi daga tuhumar hukuncin kisa, ya daukaka karar kokarin sake wata sabuwar shari’ar da za a yi masa, a kan wancan zargi da aka tuhume shi, amma aka sallame shi.
PREMIUM TIMES a ranar Litinin din nan ta samu kwafe-kwafen daukaka karar.
Daukaka karar dai fanni biyu ce. Wato na farko ya na so a sake shi, tunda har Babbar Kotun Kano ta yi fatali da hukuncin Babbar Kotun Shari’a ta Kano.
Sai fanni na biyu kuma shi ne jayayyar da ya ke yi cewa babu dalilin da zai sa a yanke wa Sharif Hukuncin kisa a karkashin wata shari’ar da ba ta kundin tsarin dokokin Najeriya.
Sannan kuma ya ce, ita kan ta dokar ta Najeriya, babu hurumin yanke hukuncin kisa a kan wanda aka zarga da yin ridda a cikin ta.
A ranar 21 Ga Janairu dai ne Babbar Kotun Kano ta soke hukuncin kisan da aka yanke wa Sharif Aminu a Babbar Kotun Shari’a.
Tun dai cikin watan Agusta, 2020 ne aka yanke masa hukuncin kisan.
Sai kuma daukaka karar da lauyan Sharif ya yi zuwa Babbar Kotun Kano, ya shaida wa kotun cewa Babbar Kotun Shari’a ta Kano ta yi haramben hukunci wajen yanke wa wanda ya ke karewa hukuncin kisa.
Sai dai kuma ita Babbar Kotun ta Kano, ta amince akwai kwange a cikin waccan shari’a da hukuncin da aka yanke, don haka sai ta ce a sake shari’ar.
Wasu alkalai biyu be dai su ka yanke hukuncin sake shari’ar, a hukuncin da su ka yanke a Babbr Kotun Kano. Alkalan sun hada sa Nuraddeen Umar da kuma Nasiru Saminu.
‘A Sake Ni Kawai, Babu Zancen Sake Shari’a’ –Inji Sharif
Sai dai kuma a cikin kwafen takardar Daukaka Karar da Sharif ya yi a Kotun Daukaka Kara ta Kano, ya ce bai amince da hukuncin Babbar Kotun Kano ba, wadda ta ce a sake shari’ar.
Ya ce tunda kotun ta riga ta sallame shi, ta soke wancan hukunci da Babbar KotuN Shari’a ta Kano ta yanke, to sakin sa kawai ya kamata a yi.
Lauyan Sharif mai suna Kola Alapinni, ya shaida wa kotun Daukaka Kara cewa, “sallamar Sharif Babbar Kotun Kano ya kamata ta yi, tunda har ta soke wancan hukuncin kisa da Babbar Kotun Shari’a ta Kano da kef Filin Hockey ta yi masa.”
Alapinni ya rika sheka ruwan ayoyi daga kundin dokokin shari’ar Najeriya, wadanda ya ce su ne hujjar cewa sallamar Sharif ya kamata a yi, ba wai a sake masa wata shari’a ba daban.
“Kundin Dokar Najeriya ya haramta a hukunta mutum sau biyu a kan laifi daya, wanda aka rigaya aka sallame shi.” Inji lauyan Sharif, mai suna Alapinni.
“Saboda haka cewa wai a sake wa Sharif wata shari’a bayan an rigaya an sallame shi, to rashin adalci ne, zalunci ne, kuma ya kauce wa dokar kundin tsarin mulkin Najeriya.” Inji lauya Alapinni.
‘Kotun Shari’a Ba Ta Ma Da Hurumi A Kundin Dokokin Najeriya’ –Lauya A lapinni
A bangare na biyu na karar da lauyan Sharif ya shigar a madadin sa, ya bayyana cewa kwata-kwata ma babu wani hurumin hukuncin kisa kan wanda ya yi ridda, bisa shari’ar Musulunci a karkashin dokar Najeriya, wato ‘constitution’.
Ya ce Babbar Kotun Kano ta tabka shirme da kuskure da rudu da kuma kasassaba da har ta ce akwai hukuncin kisa a karkashin dokar Najeriya kan wanda ya yi ridda.
“Hukuncin Shari’a Musulunci sai a kasar da ake mulkin ta bisa tsarin Musulunci ne kadai ta ke da tasiri, amma ba a karkashin gwamnatin dimokradiyya ba.” Inji lauya.
Lauya ya ce gaba da kare wanda ya ke karewa cewa ita kan ta dokar jihar Kano ta shari’ar Musulunci ta shekara ta 2000, ta kauce wa dokar Najeriya, kasar da ake dimokaradiyya, ba tsarin musulunci ba.
Alapinni ya yi ta kokarin yanko ayoyi daga cikin kundin dokar Najeriya, ya na kafa hujja da su.