Hukumar Bunkasa Noma da Raya Gonaki ta Najeriya, NALDA, ta bayyana shirin daukar masu digiri har matasa 30,000 aiki a fadin kasar nan.
Ta ce gwamnatin tarayya ta rattaba hannun amincewa a dauki matasan domin bunkasa harkokin noma da kuma wadanda za a dauka domin inganta dabarun kimiyya.
Daukar ta su inji NALDA ya zama wajibi domin su ne za su yi aikin gwajin ni’imomi da albarkar kasar noma, tare da bayar da shawarwari ga manoma a karkashin Shirin Bunkasa Matasa Manoma da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a cikin Nuwamba, 2020.
Shugaban Hukumar NALDA, Paul Ikonne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai dangane da ayyukan da ke gaban hukumar sa.
Ya ce tun farko dama idan ana so a cimma nasarar bunkasa noma, sai an yi bincike da gwajin kasar noma idan ta cancanci a shuka abin da ake bukatar shukawa a wurin ko kuma a san me ya kamata a shuka a gonar.
“Ba za mu iya samar wa kasar nan wadataccen abinci ba, har sai mun fahimci irin kowace kasa ko gonar da ya kamata a shuka kowane nau’in abinci tukunna.
“A kan haka ne Shugaba Muhammau Buhari ya amince NALDA ta dauki matasa 30,000 domin yin aikin nazarin kasar gonaki da kuma yin gwajin irin shukawa a wurin da ya kamata a shuka abin da ya dace a shuka a wurin har a samu sakamakon amfani gona sosai. Wannan kuwashi ne tushe da ginshikin noma baki daya a kasar nan.”
Kwanan nan ne wannan hukuma ta kaddamar da Shirin Bunkasa Matasa Manoma wato National Young Farmers’ Scheme, domin daukar matasa 1,000 daga kowace karamar hukuma 774 aikin gona a kasar nan. Ikonne ya ce za a bai wa masu digiri din horo na makonni biyu.
Kuma za a rika biyan kowanen su naira 500 a duk sakamakon gwaji daya na kasar noman da ya dauko.