SHUGABAN KASA 2023: Kakakin Jihar Kogi ya fara kamfen ga ‘yan majalisar Najeriya su mara wa Yahaya Bello baya

0

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi, Mathew Kolawole, ya fara bibiyar ‘yan majalisa na fadin kasar nan, domin su mara wa Gwamna Yahaya Bello na Kogi baya idan ya fito takarar shugabancin kasa a 2023.

Kolawole ya yi wannan bayanin a lokacin da ya kai ziyara a Kakakin Majalisar Jihar Filato, Abok Ayuba tare da sauran ‘yan majalisar jihar, domin neman goyon bayan su.

Kolawole ya kai ziyarar ce tare da rakiyar mataimakin sa, Ahmed Mohammed da kuma wasu ‘yan majalisa daga jihar ta Kogi.

“Makasudin zuwan mu Jos shi ne domin mu taya Kakakin Majalisar Filato Abok Ayuba, murnar zaben sa da aka yi Shugaban Kungiyar Kakakin Majalisar Jihohin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

“Sannan kuma mun zo ne domin mu kawo maku kokon barar mu na neman goyon bayan ku ga Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello, wanda shi ne mafi karancin shekaru a cikin dukkan gwamnonin kasar nan, domin ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

“Yin la’akari da kusancin mu da Gwamna Yahaya Bello a matsayin mu na ‘yan Majalisa ya sa mun tattara dukkan ayyukan ci gaban da ya samar a Kogi, ciki har da bunkasa rayuwar matasa da inganta jiha.

“To sai muka ga cewa lallai tabbas gwamnan mu ya cancanci tsayawa takarar shugabancin kasa, kuma ya cancanci shugabancin Najeriya a 2023.

“Don haka mu dai mun gamsu da shi, kuma mun amince masa. Mun zartas da kudirin cewa mu na so ya fito takarar shugabancin kasa domin ya jagoranci Najeriya.

“Hatta matasan Najeriya su ma su na ta matsa masa lamba cewa ya fito takarar shugaban Najeriya. Kuma ya amince zai fito.” Inji Kolawole.

Ya ce sun kai wannan sako ne a jihar Filato, kasancewar ta daya daga cikin jihar da APC ke mulki kuma ta na da rinjaye.

Kolawole ya ce ya yi amanna ‘yan majalisar kasar nan su sama da 900, wadanda 600 duk ‘yan APC ne, to kowanen su ‘daliget’ ne mai zabe a ranar zaben fitar da gwanin takarar shugabancin kasa a karkashin APC.

A na sa jawabin, Ayuba ya ce majalisar jihar Filato za ta goyi bayan Bello matsawar ya buga misalign adalci ya bai wa Majalisar Kogi ‘yancin cin gashin kan su.

Share.

game da Author