Jami’an tsaro 10,000 za su sa ido a zaben Kano

0

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kano ta kebe jami’anta 10,000 domin kula da zaben kananan hukumomin da za a yia jihar Kano.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Alhamis a Kano.

Haruna ya ce daga cikin jami’an tsaron akwai ‘yan sanda 7,251 sannan sauran 2,000 din da suka rage akwai jami’an sibul difens NSCDC, Jami’an kwastam NCS, Jami’an hukumar kula da shige da fice NIS, jami’an hukumar kurkuku NCoS da dai wasu jami’an tsaron kasa.

Za a tura jami’an tsaron a duka rumfunan zabe da ke jihar a lokacin zaben.

Share.

game da Author