Sarakunan gargajiya na yi wa kokarin samar da zaman lafiya a Zamfara zagon kasa – Matawalle

0

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya zargi wasu sarakunan jihar da bai bayyana sunayensu ba da yin zagon kasa ga kokarin samar da zaman lafiya da gwamnatin sa ke yi a jihar.

Gwamnan, a wani taro da shugabannin hukumomin tsaro a jihar a ranar Alhamis, ya ce sarakunan ba su taka rawar da ya kamata su taka wajen yaki da ‘yan fashi a jihar.

Ya ce hakan ya haifar da tabarbarewar rashin tsaro a jihar kwanan nan.

Taron ya kuma samu halartar malaman addini, sarakunan gargajiya da ƴan jarida a gidan Gwamnati da ke Gusau.

Gwamna Matawalle ya ce wasu sarakunan gargajiya na taimaka wa haramtattun kungiyoyin ƴan banga a yankunan da suke, abin da ya ce yana haifar da hare-haren ɗaukar fansa daga ƴan fashi.

Gwamnan ya kuma yi Allah wadai da wasu kalaman da shugaban majalisar sarakunan gargajiya na jihar, Sarkin Anka, Attahiru Ahmad yayi, inda ya ƙalubalanci gwamnatin jihar da ta baiws mutane damar mallakar makami don kare kansu, tunda gwamnatin ta gaza wajen kare su.

Gwamnan ya ce “Abin takaici ne a ce wai babban sarki kuma shugaban sarakunan jiha yana fadan irin wadannan kalamai, har da ingiza mutane su dau makamai,sannan kuma da fadin cewa gwamnati ta gaza duk da kokarin da ta ke yi a jihar.

Matawalle ya ce idan sarakunan jihar na ganin abinda ya ke yi ba su so, a shirye yake ya hakura shima don ya faranta musu rai

Share.

game da Author