Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina na damke wani malami, kuma mataimakin shugaban makarantar ‘Community Day Secondary’ dake Kadandami a karamar hukumar Rimi jihar da ake zargi ya dirka wa ddalibarsa mai shekara 12 ciki.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta gabatar da mataimakin shugaban makarantar Ibrahim Sale mai shekaru 38 tare da wasu masu aikata fyade da aka kama a jihar ranar Laraba.
Sakamakon bincike da aka yi ya bankado yadda Malam Sale ya rika tilasta wa wannan daliba yana lalata da ita har tsawon wata 8 ba tare da an sani ba, sa nan kuma an gano a gidansa yake lalata da wannan yarinya inda matan sa uku ke zama.
Bayan haka kuma bincike ya nuna yakan dan yi mata ihsani na kudi, yakan bata naira N2000 zuwa N500 a duk lokacin da ya nemi yin lalata da ita.
Malam Sale ya ci gaba da saduwa da wannan yarinya har a lokacin da take da ciki, duk da ko tsawon wannan lokaci Iyayen yarinyar basu san abinda ke faruwa har lokacin da ta haihu.
Sale ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata ganin cewa akwai amana tsakanin su da iyayen yara.
Kakakin rundunar Gambo Isah ya ce Sale na cikin mutum 8 din da suka kama kwanaki biyar da suka gabata a jihar da laifin fyade.
Isah ya yi kira ga iyaye da su rika sa ido akan ya’yan su a koda yaushe.
Ya ce za a maka wadannan mutane kotu da zaran rundunar ta kammala bincike.