KORONA: Ci gaba da kulle makarantu ba zai zame wa kasar nan alheri ba – Babban Lauya

0

Babban Lauya kuma wanka ya kafa Jami’ar Afe Babalola University da ke Ado Ekiti, a Jihar Ekiti, ya bayyana cewa ci gaba da kulle makarantu barkatai kuma babu ranar budewa, ya saba wa dokar kasa, sannan kuma ba zai zame wa Nejeriya alheri ba

Afe Babalola ya yi wannan gargadin a ranar Laraba, lokacin da ya ke wa manema labarai bayani.

Ya ce ganganci ne a ci gaba da kulle makarantu ana jiran sai lokacin da korona ta wuce.

Ya ce a halin yanzu irin yadda cutar korona ke kara kamari, za a iya sake wata shekara daya cur kafin a ga bayan cutar korona a duniya.

Musamman ya fi nuna damuwa da kulle jami’o’i wadanda ya ce an ki yin la’akari da cewa su ne wuraren da ya fi kamata a maida hankali wajen binciken hanyoyin dakile cutar korona.

Ya ce jami’o’i nan ne tushen inganta rayuwar jama’a da kasa baki daya. Don haka a cewar sa, kamata ya yi a samo dabarun kauce wa kamuwa da cutar a jami’a, maimakon a kulle su babu ranar budewa.

Ya ce irin yadda wannan dabara da Najeriya ta dauka ta bambanta da dabarun da kasashe masu tasowa ke ci gaba da dauka.

A kan haka ya ce hanyar da Najeriya ta don kauce wa korona, ta saba wa doka, ba mai bullewa ba ce, kuma ba za ta zame wa kasar nan alheri ba.

Babalola ya yi wannan bambamin ne a matsayin raddi ga bayanan Ministan Ilmi, Adamu Adamu, wanda ya ce ba zai yiwu a sake bude makarantun kasar nan a ranar 18 Ga Janairu ba, ganin yadda korona ke ci gaba da karuwa a cikin kasar nan.

Babalola, wanda lauya ne mai matsayin kololular lauyoyi (SAN), ya ce matakin da Najeriya ta dauka zai gurgunta harkar ilmi a kasar nan musamman a makarantu masu zaman kan su, wadanda ba na gwamnati ba.

Daga nan ya shawarci gwamnatin tarayya da cewa kada ma ta tsaya yin wata tababa, ta gaggauta sake bude makarantun kasar nan a ranar 18 Ga Janairu kawai.

Sannan ya roki gwamnati ta yi koyi da kasashen Turai, wadanda su ka rika biyan albashin malaman jami’o’i masu zaman kan su a lokacin da makarantun ke kulle saboda annobar korona.

Share.

game da Author