Yadda Gwamnatin Najeriya ta raba irin shinkafa ga kamfanoni 20 cikin 2020

0

Yayin da gwamnatin Najeriya ke ta kokarinn bunkasa noman shinkafa, a cikin 2020 Ma’aikatar Harkokin Noma da Raya Karkara (FMARD), ta raba irin shinkafa ga kamfanoni 20 da ke fadin jihohi 36 na kasar nan har da Abuja.

Shekaru biyu kenan da Najeriya ta haramta shigo da shinkafa daga waje, da nufin bunkasa noman shinkafa a cikin kasar nan.

Wannan aikin rabon irin shinkafa, ya na kunshe ne a cikin wani kundin bayanan harkokin noma, wanda ya fado hannun PREMOUM TIMES a ranar Litinin.

Cikin 2017 a Najeriya an noma samfarerar shinkafa har metric tan milyan bakwai. Wannan adadin kuwa ba a taba noma shinkafa mai yawan sa a kasar nan ba tun daga

A cikin watan Agusta, 2019, gwamnatin Najeriya ta rufe dukkan kan iyakokin kasar, watanni uku kacal bayan ta sa hannu kan Yarjejeniyar Cinikayya Kai-tsaye Tsakanin Kasashen Afrika.

Dalilin rufa kan iyakokin don a dakile safarar fasa-kwauri tsakanin kan iyakokin Jamhuriyar Benin, Nijar da Kamaru. Sannan kuma don a bunkasa noman wadataccen abinci a cikin kasa.

Tsarin raba irin noma na shinkafa da sauran nau’o’in kayan abinci ya na karkashin Shirin Gwamnatin Shugaba Buhari na ATP 2016-2020.

Sai dai kuma an tsara yadda shirin zai fara ne daga 2016 zai karkare cikin 2020, wato shekarar da ta gabata kenan.

Shirin ya ta’allaka ne wajen samar da kayan noma na zamani, kudade ga manona, wayar da kai da kirkirar fasaha da dabarun noma na zamani da samar da tasirin kasuwa ga harkokin tasarifin amfanin gona.

Kundin bayanan irin yadda aka raba wa kamfanoni 20 irin shinkafa ya nuna cewa an raba masu tan 1.4.

Wato kenan kowane kamfanin ya samu kilogiram 700 na irin irin shinkafa; buhu 14 mai nauyin kilogiram 50 kowane buhu.

Kundin bayanan ya nuna kamfanoni 13 a yankin Arewa maso Yamma su ke. Sai kuma kamfanoni shida a yankin Arewa ta tsakiya. Daya a Kudu maso Gabas daya kuma a Arewa maso Yamma.

Daga cikin kamfanoni 13 da ke Arewa maso Yamma, hudu a Kaduna su ke, biyar kuma a Kano, sai daya a Jigawa, daya a Zamfara, daya a Kebbi daya kuma a Katsina.

A Arewa ta Tsakiya kuwa, kamani daya a Filato, daya a FCT Abuja, daya kuma a Nasarawa, daya a Jihar Neja.

Jihar Abia ce kadai ta samu daya a jihohin Kudu maso Gabas.

PREMIUM TIMES ta tuntubi wasu kamfanonin, kuma sun tabbatar mata cewa sun samu wannan irin shinkafa daga Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Kamfanin Balue Seed Ltd Kaduna, George Zangi, ya tabbatar da karbar kilogiram 700 na irin shinkafar, wato buhu 14 kowane mai nauyin kilogiram 50.

Shi ma Shugaban Maslaha Seeds Nigeria da ke Zamfara, ya tabbatar da karbar na sa kason na irin shinkafa samfurin faro 66 da faro 67.

Share.

game da Author