Mataimakin gwamnan jihar Benuwai Benson Abounu ya bayyana cewa gwamnati ta saka dokar hana walwala a kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum a dalilin rashin tsaro da ake fama da shi a kananan hukumomin.
Abounu ya sanar da haka ranar Laraba bayan ganawa da yayi da jami’an tsaron jihar a garin Makurdi.
Ya ce saka dokar hana walwala a wadannan kananan hukumomi ya zama dole ganin yadda yin garkuwa da mutane, fashi da makami, sace-sace ya tsananta a wadannan wurare.
“Dokar za ta fara aiki daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safiya.
Bayan haka Abounu ya ce gwamnati ta hana amfani da baburan hawa a wadannan kananan hukumomi.
“Za a iya amfani da baburan ne idan za a kai mai ciki ko wani mara lafiya asibiti.
Jihar Benuwai na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Ba tun yau ba, an yi ta artabu tsakanin manoman jihar da fulani makiyaya a dalilin rashin jituwa a tsakanin su da ya tsananta.