An kashe ‘yan bindiga da Boko Haram 158 cikin sati uku – Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akalla an jami’an tsaro sun kashe ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram 158 cikin watan Janairu na sabuwar shekarar nan da mu ke ciki.

Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai a ranar Litini a Abuja.

Ministan ya ce wadannan adadin ba su cikin adadin wadanda Boko Haram ne da ’yan bindiga da aka ragargaza a farmakin jiragen yaki.

A wurin ganawa da manema labarai din har da Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, ina aka yi bayanin ci gaban da Najeriya ke kara samu wajen yaki da ta’addanci da kuma ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Lai ya ce an kuma kama rikakkun masu laifi 52 tare da kama muggan makamai da albarusai.

Ya kara da cewa an ceto mutane 17 daga hannun masu garkuwa da mutane accikin wadannan makonni uku na cikin watan Janairu.

Ya ci gaba da lissafin kayan da aka kwato daga hannun miyagun mutane masu satar kayyaki da su ka hada da gangar danyen mai 684,856, sai litar gas 1,724,000 da litar kananzir 500,000 a y ace duk na sata ne aka kwato.

Minista ya ce mahara 118 aka kashe a Yankin Arewa maso Yamma, kuma a can aka ceto wadanda aka yi garkuwa da su har mutum 11.

“An kuma kwato dabbobi 358 da makamai biyar daga masu garkuwa da mutane.

Lai ya rika bayani dalla-dalla na yawan Boko Haram da aka kashe a artabu daban-daban da kuma yawan kayan yakin su da sojojin Najeriya su ka kwato duk a cikin watan Janairu.

Sannan ya yi bayanin irin nasarorin da aka samu kan ‘yan bindigar da aka rika bude wa wuta a dajin Kaduna sau da dama.

Ya ce an samu gagarimar nasara a kan masu garkuwa da mutane, ta hanyar farmakin da aka kai masu da jiragen yaki a Dajin Chikwale da ke yankin Mangoro, cikin Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Ya ce an samun wannan gagarimar nasara a kan su a ranar Asabar lokacin da aka yi masu rubdugun hare-hare da jirgin yaki.

“An kai masu gagarimin harin ne bayan da aka samu wani rahoton sirri na inda sansanin masu garkuwa ya ke a cikin Dajin Chikwale, wanda ke tazarar kilomita 20, yamma da babban titin Kaduna zuwa Abuja.”

Da ya koma kan yankin Kudu maso kuwa, Lai ya ci gaba da lissafin kayan da aka kwato daga hannun miyagun mutane masu satar kayyaki da su ka hada da gangar danyen mai 684,856, sai litar gas 1,724,000 da litar kananzir 500,000 a ya ce duk na sata ne aka kwato.

Bayan ya kammala bayani kan buhunan takin zamani 1,184 wadanda ya ce an kama a kan iyakar Najeriya da Kamaru bayan an shigo da su Najeriya, Minista Lai ya kora bayani kan yankin Kudu maso Yamma, inda ya ce Sojojin Operation AWATSE sun tarwatsa gungun masu tace mai tare da kama kananan jiragen ruwa takwas.

Ya yi kiran jama’a su rika bayar da hadin kai ga jami’an tsaro wajen kokarin da ake yin a dakile ta’addanci da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.

Share.

game da Author