AIKI SAI MAI SHI: Yadda Yahaya Ahmed ya gina katafaren gida mai daki uku da robobin shan ruwa

0

Masu iya magana sun ce aiki sai maishi, domin kuwa ga wani Injiniya ami suna Yahaya Ahmed da aya gini katafaren gida mai daki da robobin shan ruwa da aka tsin to su a bola.

Yayaha direckta ne a wata kungiya mai zaman kanta mai suna Developmental Association of Renewable Energies in Nigeria (DARE) a Kaduna.

Gogan naka ya bayyana wa ‘yan jarida cewa robobi ya rika sa masu aikinsa suna tsinto masa ana cika su da kasa, daga nan sai ya rika gini da su har ya gina gida mai daki uku da bayi daya da dakin dafa aninci, wato kicin.

” Wannan gida da kuke gani zai yi dadewar gaske, akalla shekara 300 a tsaye babu abinda zai same shi. Sannan kuma bindiga ba za ta huda shi, Ruwa ba zai rusa shi ba kai harta girgizan kasa ba ya yi masa komai.” Inji Yahaya.

Ya ce duka matashin da ke da kwarewa a harkar gine-gine zai iya koyan yadda ake gina irin wannan gida sannan kuma tana da saukin ginawa.

” Baza ka kashe kudi masu yawa ba. robobi kawai za aka rika tarawa ana cika su da kasa, kai kuma kana shimfida gini abinka. Nakoyar da matasa da dama a kasashe dabam na Afrika.

A karshe ya ce wannan abu zai taimaka wajen sama wa mutane musamman matasa aikin yi.

Share.

game da Author