‘Yan luwadi sun fi kamuwa da Kanjamau fiya da mata – Likita

0

Likitoci sun ce maza dake luwadi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cututtuka musamman kanjamau fiye da mata masu yin madigo.

Wadannan rukunin mutane na cikin hadarin kamuwa da kanjamau ne saboda yadda suke saduwa ta dubura inda da dama daga cikin su basu amfani da kororo roba.

A Najeriya kwatan mazan dake harkan luwadi sun kamu da kanjamau sannan da dama daga cikin su basu da masaniya ko kuma sun sani amma kuma sun boye haka saboda gudun kada hukuncin dokar hana luwadi ta hau kansu.

Likitoci sun bayyana wasu dalilai da suka sa mazan dake luwadi cikin hadarin kamuwa da kanjamau.

1. Rashin yin gwajin cutar

Rashin yin gwajin kanjamau na daya daga cikin matsalolin dake kara yada kanjamau a kasar nan inda da dama daga cikin mazan dake harkan luwadi basu da masaniyar mahimmancin yin gwaji domin sanin matsayinsu.

2. Yin jima’i ta dubura

Yin jima’i ta dubura na daga cikin hanyoyin da ake kamuwa da cututtuka kamar sanyi da kanjamau.

3. Kamuwa da cutar sanyi

Yin jima’i ta dubura na sa a kamu da cutar sanyi da kanyi sanadiyyar rayuwat

4. Rashin sani

Da dama cikin mazan dake luwadi da juna basu da masaniyar cewa an fi kamuwa da kanjamau idan ana saduwa ta dubura.

A dalilin haka da dama daga cikin su ke mutuwa saboda kamuwa da kanjamau.

5. Rashin amfani da kororo roba

Share.

game da Author