Hukumar zabe ta bayyana ranar 8 ga watan Disamba, ranar da za a sake zaben ‘Inkonkulusib’ a jihar Zamfara.
Idan ba a manta ba malamin zaben farfesa Ibrahim Magawata ya ce zaben bai kammalu saboda an samu rumfunan zabe 14 da aka soke su.
Farfesa Magawata, wanda shine malamin zaben cike gurbi da aka yi a kananan hukumomin Bakura da Talatan Mafara ya bayyana cewa wannan zabe bai kammalu ba.
Sakamakon zaben da aka yi ya nuna cewa kuri’un da aka soke a rumfuna 14 sun zarce yawan banbancin yawan kuri’un da wanda yayi nasara ya samu.
Takara na APC ya samu kuri’u APC 16,464, PDP kuma kuri’u 18,645 inda ya nuna cewa dan takara na PDP ne yayi nasara a zaben amma kuma sai an sake a wasu rumfunan saboda da kuri’u 2,181 ya ba dan APC rata.
farfesa Magawata ya ce a wasu rumfunan ma ko kri’a daya ba a jefa ba saboda yan iska sun arce da akwatinan zaben.
Saida kuma an ruwaito yadda gwamnan Jihar Bello Matawalle da tsohon gwamna, AbdulAziz Yari suka yi ta cacan baki.
A shirin yin zaben cike gurbi a mazabar Bakura da Talatan Mafara wanda za ayi ranar Asabar, magoya bayan manyan jam’yyun Najeriya biyu, APC da PDP sun goge raini a garin Bakura.
Akalla mutum biyu ne aka kashe sannan wasu da dama sun arce da muggan raunuka a jikin su a dalilin harbin bindigogi da hasalallun matasan suka rika yi wajen kare jam’iyyar su.
Sai dai bayan haka gwamnan jihar ya saka dokar hana walwala a kananan hukumomin Bakura da Talatan Mafara.
Tun kafin taron kamfen din da ya ta da jijiyoyin wuyan magoya bayan jam’iyyun, Gwaman jihar Bello Matawalle ya yi gargadi da korafin cewa Ƴan APC na cakalar ƴan PDP.
Sannan yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya sa a binciki musabbabin tada zaune tsaye da ya faru a Bakura sannan kuma da hukunta wadanda aka samu da laifi.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsaida da ranar Asabar don zaben cike gurbi na kujerar Majalisar Dokoki ta jihar, inda jam’iyyu 14 ke fafatawa.
Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa magoya bayan jam’iyyar PDP mai mulki da kuma jam’iyyar adawa ta APC sun yi artabu wajen ko wanne cikinsu zai yi kamfen a filin taron dake hedikwatar karamar hukumar da ke garin Bakura.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Usman Nagogo, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa 14 da ke halartar zaben maye gurbin da su ja wa magoya bayansu kunne sannan su lallashe tunda wuri domin a cewar sa rundunar ba za ta yi kasakasa ba wajen hukunta duk wanda ya nemi ta da zaune tsaye a lokacin zaben cike gurbin da za ayi ranar Asabar.
Discussion about this post