Jakadiyar kasar Amurka a Najeriya Mary Leonard ta bayyana cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya wajen yaki da cutar.
Mary ta fadi haka ne a taron inganta sanin yawan mutanen dake dauke da cutar da aka yi a Abuja a makon jiya.
Ta ce gwamnatin kasar ta bai wa mutum miliyan 1.2 maganin kanjamau da tarin fuka.
Sannan gwamnatin ta tallafa wajen bai wa yara miliyan 1.3 maganin cutar a kasar nan.
“Kanjamau ta zama annoba a kasar nan domin cutar ta kashe mutum sama da 690,000 a shekaran 2019.
“A dalilin haka gwamnatin ta inganta Samar da maganin cutar domin ceto rayukan mutanen da suka kamu da cutar.
Mary ta Kuma ce duk da fama da aka yi da annobar korona gwamnatin Amurka da asusun PEPFAR sun samarwa mitane da tallafi a Najeriya.
“Sannan za mu ci gaba da hada hannu da gwamnati da mutanen Najeriya domin ganin an dakile yaduwar cutar a kasar kwatakwata.
Daganan sai Mary ta ce Amurka ta kashe dala biliyan 85 wajen dakile yaduwar kanjamau daga 2003 zuwa 2020 a Najeriya.
Ta ce hidiman da kasar Amurka ta yi ya taimaka wajen ceto rayukan mutum miliyan 17 a Najeriya.
“A shekarar 2020 Amurka ta taimaka wajen yi wa mutum miliyan 8.2 gwajin cutar sannan an yi wa mata masu ciki miliyan 1.2 gwajin kuma an wayar musu da Kai Kan yadda za su iya kare jariran dake cikinsu daga kamuwa da cutar sannan da wayar da kan mata masu ciki hanyoyin kariya daga cutar.