‘Yan bindiga sun sace babban limamin Darikar Katolika

0

Wasu mahara sun arce da babban Bishop din Darikar Katolika na Owerri, babban birnin Jihar Imo.

An sace Moses Chikwe ne a ranar Lahadi tare da dereban sa, wanda ba a ambaci sunan direban ba.

Amma daga bayan an tsinci motar babban limamin tare da alkyabbar sa daidai kusa da wani babban coci na Asusumpta Cathedral a Owerri.

Wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Darikar Katolika ta Najeriya, wadda Babban Bishof Victor Obinna ya fitar, ta tabbatar da sace babban limamin na Owerri.

Sakataren Hedikwatar Katolika ta Kasa, Zacharia Sanjumi ya yi kira a ci gaba da addua’a ubangiji ya kubutar da shi lafiya.

Ko a ranar 15 Ga Disamba, an sace wani limamin Kirista mai suna Valentine Ezeagu a garin.

Dukkan wadannan garkuwa biyu dai ba a yi bayanin shin Fulani makiyaya ne su ka sace su ko ’yan iskan gari ba.

Har zuwa rubuta wannan labari dai wadanda su ka yi garkuwa da shi, ba su kira ba, ballantana a san halin da ya ke ciki, ko kuma a san adadin kudin diyyar da su ke bukatar karba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda mahara sun arce da ango da amarya, bayan sun kashe kawun dan majalisa

“Duk fa wannan rashin mutunci da rashin tausayin da aka tafka, akwai jami’an tsaro a kusa da inda ‘yan bindigar su ka kashe kawu na.” Haka Dan Majalisa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wannan kisa da garkuwa sun faru ne a yankin Runka, cikin Karamar Hukumar Safana a Jihar Katsina, inda mahara su ka arce da amarya da ango, bayan sun bindige kawun Dan Majalisar Jihar Katsina, mai wakiltar Karamar Hukumar Safana.

Mazuna yankin sun shaida cewa abin ya faru a cikin Runka, inda mahara su ka kashe Sama’ila Supa, wanda kawu ne da Abdullahi Haruna, Dan Majalisa mai wakiltar Safana, a Jihar Katsina.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES, Honorabul Haruna ya ce an bindige kawun sa ya mutu bayan ya ki yarda a tafi da shi.

“Duk fa wannan rashin mutunci da rashin tausayin da aka tafka, akwai jami’an tsaro a kusa da inda ‘yan bindigar su ka kashe kawu na.” Haka Dan Majalisa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Ya ce tsakanin wurin da aka kashe kawun sa da inda jami’an tsaro su ke, bai wuce kilomita biyar ba, amma haka a kullum a yankin na su masu gakuwa ke shigowa su yi rashin mutunci, ku kama wanda su ka ga dama, su shiga daji da shi.

“Babu ranar da masu garkuwa ba za su shiga yankin mu su yi garkuwa da mutnae ba. Ko jiya da dare ma sun shiga garin Babban Duhu, su ka arce da mutum 13, amma daga baya bakwai su ka tsere da kyar, su ka kubuta. Sun kuma harbi mutane da dama, wadanda yanzu haka duk su na asibiti a kwance, ana kula da su.”

Limamin Masallacin Izala na Runka, Malam Yakubu, bayan ya yi wa gawa sallah, ya roki shugabanni su ji tsoron Allah, su tashi tsaye su kare rayuka da dukiyoyin talakawan su.

Sannan kuma ya ce ya kamata kowa ya tashi ya kare kan sa, domin a same ka a kashe, har gar aka mutu wajen kare kan ka.

Ita kuma amarya da angon ta da aka gudu da su, an sace su ne ranar Litinin, mako daya kacal da daura masu aure.

An bayyana sunan angon Sama’ila Abdullahi, ita kuma amaryar Zainab Isma’il.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa jami’ai na bakin kokarin su domin su kubutar da wadanda aka yi garkuwar da su.

Share.

game da Author