JARUMA: Yadda macen da ke sana’ar cire kudi da aikawa ta (POS) ta kwace bindigar ’yan fashin da suka zo mata sata

0

Wata jarumar mata da ke tsaron Asusun Cirar Kudi (POS), mai suna Ann, ta yi abin bajinta da jarumta, inda ta kwace bindiga a hannun wasu ‘yan fashi da su ka ritsa ta, domin su kwace ilahirin kudaden da ke cikin shagon ta.

Lamarin ya faru a Uhogua, cikin Karamar Hukumar Ovia Arewa-maso Gabas a Jihar Edo.

Wannan unguwa da ke kusan karshen garin Benin Babban Birnin Jihar Edo, a can ne Gidan Marasa Galihu Da Masu Gudun Hijira su ke, kusan su 3,000.

PREMIUM TIMES ta gano cewa ita wannan mata mai suna Ann, a kofar shiga gidan masu gudun hijira din ta ke tsaron shagon cira da tura kudade a saukake, wato POS, wanda a Turance aka fi sani da ‘Point of Sale.’

’Yan fashin dai sun same ta inda su ka ciro katin cirar kudi, wato ATM card, su ka ce mata ta ciro masu naira 200,000.

Sai dai kuma nan da nan jikin Ann ya ba ta cewa mutanen biyu barayi, ba masu cirar kudi ba ne.

Wani da aka yi abin a gaban idon sa mai suna Obukohwo Omatshola, ya bayyana cewa wajen karfe 4 na yammacin ranar Litinin ce barayin su ka isa wurin, su ka nemi a ciro masu naira 200,000.

“Yayin da matar ke kokarin fara daddanna POS domin tabbatar da ATM card din su, sai kawai su ka ciwo wata bindigar gargajiya, su ka nemi ta ba su dukkan kudaden da ke wurin ta.

“Matar nan da ta yi kukan kuran-kura ta ki kumumuwa, sai ta rarumi bindigar daga hannun dan fashin, ta bige bindigar daga hannun sa, kuma ta kwartsa ihu. Jami’an tsaron da ke kusa kuwa su ka garzayo, aka yi tara-tara aka damke su.

Majiyar ta bayyana sunan barayin biyu Andrew Adubu da Destiny Olu. Sun je wurin ne a kan wani babur na okada.

Sun shaida wa jama’a kafin a damka su hannun ‘yan sanda cewa sun nemi yin fashin ne domin sayen kayan abinci a wannan lokacin zaman hutun bukukuwan sabuwar shekara ga iyalan su.

Baya ga bindigar da aka samu a hannun su, shi ma babur din da aka kama tare da su ba shi da lamba ballantana rajista.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da lamarin. Ya kori jama’a su ka kai rahoton batagari. Sannan kuma ya ce za a maka su kotu domin a hukunta su da zarar an kammala bincike.

Share.

game da Author