Yayin da bilyoyin jama’a a duniya ke addu’ar kada Allah ya maimaita abin da ya faru a shekarar 2020, shi kuwa mashahurin dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski, ko shakka babu ba zai fasa yin addu’ar Allah ya rika maimaita masa abin da ya faru da shi a shekarar 2020 ba.
Hakan kuwa na da nasaba ne da irin daukakar da ya samu a duniyar kwallon kafa cikin 2020, wadda babu wani dan wasa da ya samu ko kusan irin ta sa a wannan shekarar.
Ga jerin nasarorin da Lewandowski ya samu a cikin 2020:
Cin Kofin Bundesliga na Jamus
Lashe Kyautar DFB Pokal
Cin Kofin Champions’ League
Lashe Kofin DFL Super Cup
Cin Kofin UEFA Super Cup
Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Turai
Cin Kyautar Gwarzon Dan Gaba Na Turai
Lashe Kyautar Wanda Ya Fi Kowa Cin Kwallaye Bundesliga
Cin Kyautar DFB Pokal ta Wanda Ya Fi Cin Kwallaye
Lashe Kyautar Wanda Ya Fi Cin Kwallaye a Gasar Champions’ League
Cin Kyautar Wanda Ya Fi Cin Kwallaye a Duniya a 2020
Gwarzon Dan Wasan Bayern Munich Na Shekara
Gwarzon Dan Wasan Jamus Na Shekara
Gwarzon Dan Wasan Shekara na AS
Gwarzon Dan Wasa Na Mujallar World Soccer Na Shekara
Gwarzon Dan Wasa Na Tuttosport Na Shekara
Gwarzon Dan Wasa Na Mujallar FourFourTwo Na Shakera
Gwarzon Dan Wasan FIFA Namiji Na Shekara
Gwarzon Gwarazan Kowane Wasa Na Turai Na Shekara
Gwarzon Kyautar Globe Soccer Na Shekara
Gwarzon Duk Duniyar Kwallo Na Shekara